Sojojin Nijeriya sun kashe wasu kwamandojin Boko Haram a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu hare-hare ta sama da dakarun sojin Nijeriya suka kai ranar 20 ga watan Disamba a ƙauyen Mantari an yankin Gezuwa da ke cikin ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Nijeriya ya yiisanadin kashe wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin sama na ƙasar Air Commodore Edward Gabkwet ya sanya wa hannu ya ce harin ya yi sanadin mutuwar manyan kwamandojin qungiyar da suka haɗar da Khaids Abbah Tukur da Maimusari da kuma Bakura Jega, tare da wasu ‘yan ƙungiyar da dama.

Labarin ya fito ne jim kaɗan bayan da manyan hafsoshin sojin ƙasa da na sama suka hallara a birnin Maiduguri ranar Lahadi da safe, domin yin shagulgulan bukukuwan Kirsimeti tare da sauran dakarun da ke fagen daga.

Sanarwar ta ci gaba da cewa dakarun sojin saman sun ƙaddamar da harin ne bayan da suka samu bayanan sirri da ke cewa wani kwamandan mayaƙan Boko Haram mai suna Ikirima, ya shirya dakarunsa riƙe da bindigogi a ƙauyen Mantari, tare da wasu ‘yan tayar da ƙayar bayan sun taru a waje guda a kan babura da kekuna.

”Nan take kuma aka bayar da umarnin ƙaddamar da hari kansu, lamarin da ya haddasa kashe manyan kwamandojin tare da wasu mayaƙan qungiyar aƙalla 100”, kamar yadda sanarawar ta bayyana.

Bayan harin ne kuma wasu daga cikin mayaƙan suka koma wajen da lamarin ya faru domin ɗaukar gawarwakin ‘yan uwansu, hakan ne kuma ya bai wa dakarun sojin damar sake far musu tare da kashe wasu da dama cikinsu.

Manyan hafsoshin sojin sama da na ƙasa na ƙasar sun yaba da wannan ƙoƙari na dakarun tare da sauran jami’an tsaro ƙarƙashin Operation Haɗin Kai, da kuma ci gaban da suke samu a yaƙin da suke yi da ƙungiyar Boko Haram.