“Masu garkuwa da mutane ke iko da wani yanki na Jihar Zamfara”

Daga SUNUSI MUHAMMAD a Gusau

A Jihar Zamfara mutum huɗu sun mutu wasu goma sun samu raunuka a garin Ruwan Baure da ke cikin Ƙaramar Hukamar Gusau bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a yammacin Litinin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu garkuwa da mutanen suka sako wasu mutane sama da 200, sai dai sun kashe wasu mutum 28 a lokacin da suka yi garkuwar da su a garin Randa da ke cikin Ƙaramar Hukumar Maru a Jihar ta Zamfara.

Wannan mutumin da BBC ta sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya shaida harin da aka kai, kuma ya ce da ƙyar ya tsira da ransa.

“Maharan sun afko wa garin bisa mashin kusan 100.”

Ya ce an dauko gawarwakin mamatan kuma ana shirin yi musu sutura, kuma rikicin ya sa wasuna kauracewa yankin.

“Ga mata can da yara suna takawa a kafa zuwa ƙasar Kwatarkwashi a karamar hukumar Bungudu. Maza ne kawai suka tsaya a garin domin a yi wa mamatan jana’iza.”

Ya koka kan rashin ɗaukar mataki daga vangaren hukumomin jihar.

“Mutanen nan an san inda suke, an san uwayensu domin ba baki ba ne. har ta kai ga ranar talata sun yanka wa mutanen Gora tara ta Naira miliyan biyu, kuma sun je garin da motar daukan kaya samfurin Canter kuma suka raba mazauna garin da buhu 130 na dawa.”

‘Yan bindiga sun sako mutum 200 da suka yi garkuwa da su a garin Randa Wannan mutumin na cikin waxanda aka sace:

“Mu 162 aka xauka daga garinmu, kuma kwananmu 20 daidai a hannunsu, sai ranar Lahadi suka sako mu.”

Ya ce masu garkuwa da su sun raba su cikin ɗakuna shida, kuma babu wanda ya san ainihin abin da ke faruwa, sai dai abin da aka gaya musu.

“Cikin waɗanda aka sace tare da ni, mutum 28 ‘yan bindigar suka kashe. Ko da yake wasunsu yunwa da wahala ce ta yi sanadin mutuwarsu.”

Amma ya ce waɗanda wuya ta sa suka mutu ba su wuce mutum uku ba, “sauran harbe su aka yi.”

BBC ta tuntuvi rundunar ‘yan sandan Nijeriya a Jihar ta Zamfara, sai dai kakakin rundunar ya ce jami’ansu na kan bincike kan wannan lamarin.

Shi ma ya koka ganin yadda ɓarayin dajin ke kai musu hari a duk lokacin da suka ga dama.

“Abin takaici shi ne babu mai iya yi musu komai, kowa ya san garin da suka mayar sansaninsu, amma babu abin da hukuma ta yi musu. Lallai na san masu garkuwa da mutanen nan ke iko da wannan yanki na Zamfara.”

“Tun da farko mun ba su miliyan shida, amma sun ce suna buƙatar mu tara musu ƙarin miliyan 30 ne. Sannan kafin wannan lokaci sun sace mana buhunan dawa fiye da 200.”