Kai ni fa na ga kamar Gwamna Ganduje Abba Gida-gida yake yi

*Anya kuwa ba zai yi riƙo da dabarun Sanata Kwankwaso da Sanata Shekarau ba ne?

Daga SUNUSI SHEHU

Salamun alaikum, abokai da ‘yan uwa masu karatu. Na yi wannan rubutu ne cike da kokonto mai tarin yawa a zuciyata, saboda ganin yadda a hasashe da nazarina, kamar Gwamna Ganduje Abba Kabir na jam’iyyar adawa ta NNPP yake yi a matsayin ɗan takarar gwamnan Jihar Kano, watau shi zai yi wa aiki a ɓoye, maimakon ɗan takarar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

Ga dukkan alamu kuma bisa ga al’adar jagororin siyasar Kano na wannan zamani, wato tun daga 1999 ba sa son jagorancin mutanensu ya kuɓuce musu, watau wani nasu, bayansu ya zama gwamna ya zama jagora. Wannan dabara ta fara daga tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso ne, yayin da a wancan lokaci na baya, ya yi dabara ya yi hikima ta yin burus da bibiyar nasarar da ɗan takararsa a 2007, Ahmad Garba Bichi, ya iya samu, don kada ya zama gwamna ya ƙwace masa Jagorancin jam’iyar daga hannunsa.

Haka nan ma Gwamna Malam Shekarau ya yi yayin da ya tsayar da Malam Salihu Sagir Takai a 2011, cikin hikima da tilasta ɗan takarar ga mutanen nasa, alamu suka nuna ya ƙi nuna damuwarsa da mayar da hankalisa ga takar ɗan takarar tasa, don kada shi ma ya zama gwamna ya karɓe masa jagorancin mutanensa.

To, yau ma idan masu hankali suka nutsa cikin duba ta tunani, za su tambayi anya kuwa, Gwamna Ganduje yana himmatuwa wajen ganin Nasiru Gawuna ya ci zaɓe, ya zama jagoran APC a Kano kuwa?

Ba lallai ba ne abin da nake tunani akai ya zama daidai, amma dai daga dukkan nazari, na san ‘yan Gandujiya ba su san ubansu ba. Kai Ina iya rantsewa ba su san Uban Abba ba. Gwamna Ganduje mutum ne mai hakuri da kawaici, kuma marar izza, amma gwani ne kuma ƙwararre sosai a wajen yin likimo kamar yadda ya faɗa da bakinsa.

Ni Ina ganin ya kamata, kuma ya dace, ‘yan Gandujiya su yi nazari sosai a irin takun uban nasu tun kafin lokaci ya qure musu. Ba wai Ina nufin za su iya gane abinda uban nasu yake nufin ya same su ba a fuskarsa ba. A’a, ina! ai ba ma za su iya ganewa ba, ai Ina yi musu rantsuwa ko Gwaggo, Mai girma Farfesa Hafsat, ba za ta iya gane gwanintar gwanin nata ba.

Gwamna Ganduje gwani ne na qin karawa, saboda tarin iliminsa da iliminsa na sanin rayuwa, don haka gane dabarunsa sai wanda ya koma baya tun kafin rigimar G7 ya yi nazarinsa sosai. Irin su Sanata kuma Madugu Rabi’u Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau mutane ne da masu nazari suna iya gane su, su yi hasashen su da wuri saboda, su hankalinsu da tunaninsu da dukkan dabarunsu suna voye ne a irin kallonsu da dabarun aiwatarwarsu, amma Gwamna Ganduje sai dai idan ka bi sawun lissafinka tun daga tushe ka harhaɗa komai za ka iya kaiwa ga tunanin yadda yake son aiwatar da munufarsa.

Lokacin da za a yi zaɓen Inkwankulusib a Ƙaramar Hukumar Nasarawa, sai aka ga Gwamna Ganduje ya je yana ɗaukar kankare a kansa, ake ta yi masa dariya wai kiɗime yana nuna damuwarsa da son mutane su san irin rudewarsa da son a ci zave ce, amma ga masu nazari sosai sun san shi ba haka ya lissafa lissafin nasa ba, abin ya wuce haka, yin hakan nasa yana ɗauke da bayanai ɓoyayyu da duniya za ta yarda da abin da za a zo da shi a ƙarshe.

A taikaice dai ba wai Ina son na ce ni na san mai girma Gwamna Ganduje ba ne, a’a, Ina dai son na san ko kai ma mai karatu, me ka ke hasashe idan Gawuna ya ci gwamna ya zama Jagoran APC a Kano?

Dukkan wannan rubutu hasashe ne, ba wai zallar gaskiya ko wani aikin bincike na ilimi da nazari ba ne, a’a. zato da tsammani ne, saboda na san filin ƙwallon buga siyasa, fili ne mai santsi da bayar da mamaki, kuma fili ne na yaudarar kowa, don cimma nasarar masu buga ƙwallon, wanda hakan ce ta sanya su kansu ‘yan siyasar su kan ce, ‘siyasa babu aboki na dundundun, kuma babu makiyi na dundundun’, watau dai babu tabbas a komai.
Bissalam, na gode.

Sunusi Shehu marubuci ne kuma mai nazarain al’amuran yau da kullum a Kano da Nijeriya.