Daga CMG HAUSA
Mai ɗakin shugaban ƙasar Sin Peng Liyuan, ta aike da sakon taya murnar bikin karrama waɗanda suka yi fice, a fannin tallafa wa ilimin yara mata da mata na bana, wanda ya gudana a jiya Talata a birnin Paris na ƙasar Faransa, karkashin jagorancin hukumar raya ilimi kimiyya da al’adu ta MƊD UNESCO.
Cikin wasiƙar, Peng Liyuan, wadda kuma ita ce jakadiyar musamman ta asusun UNESCO, mai lura da manufar ingiza ilimin yara mata da mata, ta ce alfanun samar da ilimi ga wannan rukuni na al’umma ya wuce batun bunƙasa rayuwar mata kaɗai, duba da cewa, hakan muhimmin jigo ne na ingiza ci gaba mai ɗorewa ga ɗaukacin al’ummun duniya.
Peng Liyuan, ta ce yayin taron baya-bayan nan na MƊD game da kyautata tsarin samar da ilimi, an jaddada muhimmancin ilimi wajen inigiza daidaiton jinsi, inda aka yi kira da a ƙarfafa rayuwar mata, ta hanyar samar musu da ingantacen ilimi.
Peng ta ƙara da cewa, har kullum ƙasar Sin na dora muhimmancin gaske, ga batun raya ilimin yara mata da mata, yayin da kuma ake ci gaba da inganta damar su ta shiga a dama da su, a harkokin raya tattalin arziki, da ci gaban zamantakewa da sauran su.
Mai fassara: Saminu Alhassan
