Phyna ta zama Gwarzuwar Shirin Big Brother Zango Na 7

Daga AISHA ASAS

Ijeoma Josephina Otabor wadda aka fi sani da Phyna ta yi nasarar zama gwarzuwar shahararren shirin nan na talabijin, wato Big Brother Naija zango na bakwai. Inda zata samu zunzurutun kuɗi har miliyan ɗari a matsayin kyautata ta wannan nasara.

Ijeoma dai ta kara da mutane 19 a wannan wasar, yayin da ake ɗauke ɗai-ɗai har suka rage su shida a satin ƙarshe na wannan wasan. Waɗanda suka fatata a zagaye na ƙarshe sun haɗa da Adekunle, Bella, Bryann, Chichi da kuma Daniella.

Big Brother Naija, shiri ne da aka fara gudanar da shi a ranar 5 ga watan Maris, shekara ta 2006. Waɗanda aka zava don yin wasar na kasancewa a wani keɓaɓen gida, yayin da duniya ke kallon mu’amala da kuma ababen da suke aikatawa, kuma ta hakan ne za a san wanda ya kamata ya bar shirin, wato daga ra’ayoyin mutane. 

Shiri ne da gidan talabijin na Africa Magic, M-Net ke shiryawa. Kuma zuwa yanzu an gabatar da shirin sau bakwai tun fara gabatar da shi.