Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Asusun Bunƙasa Fasahar Man Fetur (PTDF) ya buƙaci ‘yan jarida su riƙa wallafa sahihan rahotanni masu cike da gaskiya kan harkokin mai da iskar gas a Nijeriya, yayin da ya kammala wani shirin horaswa da aka gudanar a Legas domin ƙara wa ƙwararrun kafafen yaɗa labarai ilimi kan yadda ake ba da rahoto a wannan muhimmin fanni.
Shirin horaswar ya samu halartar kusan ‘yan jarida 50 da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai, inda aka koya musu dabarun fahimtar fannoni na fasaha da manufofin da suka shafi masana’antar mai da iskar gas, tare da yadda za su isar da irin waɗannan batutuwa ga jama’a cikin sauƙi da inganci.
Da yake jawabi a wajen rufe taron, Babban Sakataren Asusun Bunƙasa Fasahar Man Fetur (PTDF), Farfesa Shuaibu Shehu Aliyu, ya ce shirin wani ɓangare ne na ƙudirin asusun na inganta rahotannin da ake yi kan masana’antar mai da iskar gas ta Nijeriya.
Aliyu, wanda Shugabar Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na PTDF, Dupe Kay-Hambolu, ta wakilta, ya ce kafafen yaɗa labarai ba kawai hanyar isar da bayanai ba ne, har ila yau abokan hulɗa ne masu muhimmanci wajen wayar da kan al’umma, tabbatar da gaskiya da kuma tallafa wa ci gaban ƙasa.
Ya ce saboda sarkakiyar da ke tattare da harkokin mai da iskar gas da kuma sauye-sauyen da ake samu a kai a kai, wajibi ne ɗan jarida ya mallaki cikakkiyar fahimta game da manufofi, fasahohi da sauran muhimman batutuwan da ke tafiyar da masana’antar, ba wai dogaro da bayar da labarai cikin gaggawa kaɗai ba.
A cewarsa, a matsayin hukuma mafi girma da ke da alhakin bunƙasa ƙwararrun ma’aikata a fannin mai da iskar gas, PTDF ba ta takaita aikinta ga horas da masana kawai ba, har da tabbatar da cewa masu isar da bayanai ga jama’a sun samu isasshen ilimi kan harkar.
Ya bayyana cewa nasarorin da PTDF ta samu wajen bunƙasa ƙwararru, inganta bincike da ƙirƙire-ƙirƙire, ƙarfafa amfani da ƙwararrun cikin gida da kuma tallafa wa makomar makamashin Nijeriya na buƙatar a bayyana su cikin sahihanci, cikakken bayani da kuma amintaccen tsari.
Aliyu ya ƙara da cewa, shirin ya ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin PTDF da kafafen yaɗa labarai, yana mai jaddada cewa asusun zai ci gaba da bunƙasa wannan haɗin gwiwa ta hanyar tattaunawa, buɗaɗɗen aiki da mutunta juna.
Ya kuma buƙaci mahalarta taron su yi anfani da damar wajen yin tambayoyi, musayar ra’ayoyi da kuma amfana da ilimin da aka gabatar.
Har ila yau, ya yabawa Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na PTDF bisa ƙirƙiro da wannan shiri, tare da gode wa kamfanin BetterWays Nigeria Limited saboda haɗin gwiwar da ya bayar wajen ganin an gudanar da shi cikin nasara.
Tun da farko, Daraktan Gudanarwa na Rukunin Kamfanonin BetterWays, Dakta Victor Dare, ya bayyana cewa harkar mai da iskar gas ita ce ginshiƙin tattalin arzikin Nijeriya.
Ya ce fannin na samar da kusan kashi 65 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na gwamnati, fiye da kashi 85 cikin 100 na kuɗaɗen da ƙasa ke samu daga fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, da kuma kusan kashi 90 cikin 100 na kuɗaɗen musayar waje, duk da cewa gudunmawarsa ga jimillar tattalin arzikin ƙasa (GDP) ba ta kai kashi 10 cikin 100 ba.
A cewarsa, kasancewar Nijeriya ita ce mafi girma wajen haƙo ɗanyen mai a nahiyar Afirka, masana’antar na taka muhimmiyar rawa wajen jawo jarin masu zuba hannun jari da tsara manufofin kuɗi, amma kuma hakan na sa tattalin arzikin ƙasar ya dogara sosai kan sauyin farashin mai a kasuwannin duniya.
