Raɗɗa ya ƙaddamar da rabon buhun hatsi 90,000 ga mabuƙata a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na yaƙar yunwa da rashin abinci mai gina jiki a faɗin jihar, yana mai cewa wannan ƙalubale ba wai na siyasa bane kawai, amma nauyin ɗabi’a da na addini da dole ne a fuskance shi da tausayawa da haɗin kai.

Da yake jawabi a wajen bikin ƙaddamar da rabon buhunan hatsi 90,000 ga gidajen da ke cikin ƙunci, wanda aka gudanar yau a filin wasa na Muhammadu Dikko, Gwamna Raɗɗa ya ce wannan shiri martani ne kai tsaye ga matsin tattalin arziki da al’umma ke fuskanta da kuma ƙaruwa ta rashin abinci mai gina jiki musamman ga yara a jihar.

“Wannan taron ba wai na abinci kaɗai bane. taro ne na tausayawa, nauyi, da alhaki,” in ji Gwamna Raɗɗa. “Yana nuni da ƙudirin gwamnatin sa ne cewa babu wani iyali a Katsina da zai kwanta da yunwa, kuma babu wani yaro da zai sha fama da rashin abinci mai gina jiki ko sakaci.”

Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiri ya biyo bayan rahoton wani kwamiti na musamman da ya kafa a farkon shekarar nan domin binciken halin rashin abinci mai gina jiki a jihar Katsina. Rahoton kwamitin, a cewarsa, ya gano abubuwa masu tayar da hankali da suka buƙaci gaggawar shigar gwamnati don kare lafiyar yara da gidajen da ke cikin matsin rayuwa.

Ya ce an tantance masu cin moriyar rabon ne ta amfani da sahihan bayanai daga hukumar kula da lafiya matakin farko (PHCDA), kwamitocin al’umma, da kuma kwamiti kan rashin abinci mai gina jiki, domin tabbatar da cewa buhunan hatsi sun isa ga waɗanda suka fi buƙata.

Gwamnan ya jaddada cewa duk da cewa gwamnati tana taka nata rawa, nauyin kula da yara da kare lafiyar iyali abu ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa.

“Kula da yara ba kawai aikin gwamnati ba ne, ibada ce ta addini,” in ji shi. “Idan yaro ya kwanta da yunwa, ko uwa ba ta da abin ciyar da ɗanta, wannan ba matsalar tattalin arziki ba ce kawai — gazawar ɗabi’a ce da ta ruhaniya.”

Gwamna Raɗɗa ya kuma sanar da wasu shirye-shirye masu gudana da nufin yaƙi da rashin abinci mai gina jiki da kuma ƙarfafa tsarin kula da lafiya a faɗin jihar Katsina.

Ya bayyana cewa gwamnati tana kafa cibiyoyi 60 na Outpatient Therapeutic Programme (OTP) a sassa daban-daban na jihar don tallafawa yara da iyaye mata cikin gaggawa, sannan kuma ana inganta cibiyoyi 9 na kula da rashin abinci mai gina jiki da ke kan gaba wajen karɓar marasa lafiya domin ƙara ƙarfin aiki da inganta hidima.

Haka kuma, Gwamnan ya bayyana cewa ana shirin kafa masana’antar sarrafa Tom Brown da Ready-to-Use Therapeutic Food (RUTF) a Katsina domin samar da abincin ƙari ga yara da mata masu jinya a cikin gida.

By ukarofi