Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa harkar noma daga tushe yayin da ya ƙaddamar da rabon kayan aikin ban-ruwan noma da klkayayyakin noman zamani ga manoma a faɗin jihar.
An gudanar da wannan bikin ne a ɗakin taro na Banquet Hall da ke gidan gwamnati Katsina, ƙarƙashin shirin Katsina State Community Development Programme (CDP) tare da haɗin gwiwar ma’aikatar noma da hukumar ban ruwan Jihar Katsina (KTARDA).
Gwamnan ya bayyana taron a matsayin wani ɓangare na hangen nesa na gwamnatinsa na ƙarfafa al’ummomin karkara da daidaita noma a matsayin ginshikin tattalin arzikin jihar Katsina.
“Wannan rabon ba wai kawai rarraba kayan aiki ba ne,” in ji Gwamna. “Wani alamar haɗin kai ne wajen inganta rayuwar mutanenmu, musamman manomanmu masu ƙoƙari da suke sanya abinci a kan teburanmu kowace rana.”
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa kayan da aka raba sun haɗa da na’urorin ban-ruwan noma guda 4,000, injinunan feshi 4,000, magungunan kashe ciyawa da takin zamani mai ruwa.
Ya ƙara da cewa an kafa shirin cigaban al’umma CDP ne domin kawo gwamnati kusa da jama’a, ta yadda al’umma za su riƙa gano buƙatunsu da kansu sannan su jagoranci ci gaban yankunansu.
“Lokacin da na hau mulki, na yi alƙawari cewa gwamnati ba za ta zauna a cikin jin daɗi ba yayin da talakawa ke fama da wahala. Wannan alƙawari ne ya haifar da CDP — tsari da ke bai wa gwamnati damar sauraron jama’a kai tsaye da amsa musu bisa buƙatunsu na gaskiya,” in ji shi.
Gwamnan ya umarci hukumar CDP da ta kula da isar da kayan, sa ido da tabbatar da gaskiya wajen rabon kayan. Haka kuma ya ba da umarni ga KTARDA da ta tura masu bayar da shawarwarin noma domin su koya wa manoma yadda ake amfani da kayan yadda ya kamata.
“Waɗannan kayan mallakar manomanku ne — amma fiye da haka, mallakar makomar jihar Katsina ne. Ku yi amfani da su da hankali domin inganta amfanin gona da fitar da iyalanku daga talauci,” in ji shi.
Gwamna Raɗɗa ya gode wa ma’aikatar noma, KTARDA, tawagar CDP, ALGON, da abokan ci gaba saboda rawar da suka taka wajen tabbatar da nasarar shirin.
A nasa jawabin, shugaban CDP, Dokta Kamal, ya bayyana irin gagarumar nasarar da shirin ya cimma tun daga lokacin da aka kafa shi.
” Kusan shekara guda kenan babu wani gari a Katsina da bai amfana da CDP ba,” in ji shi. “Mun raba takin zamani a matakin rumfunan zaɓe, mun bai wa zawarawa da mata masu rauni tallafin kudi ₦50,000 ta hanyar shirin KT-Cares, kuma mun tallafa wa ƙananan manoma wajen bunƙasa noman su.”
Dakta Kamal ya ƙara da cewa a lokacin azumin Ramadan, CDP ta kai kayan abinci ga dubban iyalai ta hannun kwamitocin al’umma, kuma tana ci gaba da mayar da hankali wajen tallafawa manoman ban-ruwa da kayan aiki na zamani.
Kwamishinan Noma, Hon. Aliyu Lawal Shargalle, ya roƙi manoman da su yi amfani da kayan yadda ya kamata, tare da tunatar da su cewa ba don siyarwa aka ba su ba, don inganta noma ne da tabbatar da tsaron abinci.
“Wannan shiri zai ƙarfafa noman ban-ruwa, ya inganta samar da abinci mai ɗorewa, kuma ya ƙara ƙarfin tattalin arzikin jiharmu,” in ji shi.
