ADC ta yi tir da barazanar harin Amurka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar adawa ta ADC ta yi watsa da barazanar Shugaban Amurka, Donald Trump na ɗaukar matakin soja akan Nijeriya bisa zargin kisan kiyashi ga Kiristoci.

Haka kuma jam’iyyar ta ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gaza sauke alhakin da ke kanta na bai wa rayukan al’umma kariya.

Wannan na zuwa ne bayan Trump ya nuna damuwa kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya, inda ya yi barazanar mamaye kasar domin yaƙi da ƴan ta’adda.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa wannan barazana daga Amurka na iya jefa Nijeriya cikin mawuyacin hali, tare da raunana tsarin dimukraɗiyya da haɗin kan ƙasa.

ADC ta kuma ɗora alhakin taɓarɓarewar tsaro akan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa kusan mutane 15,000 aka kashe tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci a samu garambawul a harkokin tsaro, binciken manyan jami’an tsaro, da kuma naɗa jakadu cikin gaggawa don ƙarfafa musu gwiwa wajen daƙile ƙalubalen da ƙasar take fuskanta.

By Babaji