
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A jiya Litinin Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi alla-wadai da ikirarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels, Wike ya ce batun cewa ana yi wa wani ɓangare kisan kiyashi a ƙarƙashin mulkin Tinubu ba gaskiya ba ne.
Ya ce, babu yadda ace gwamnati ta zuba ido ana yi wa al’ummarta kisan kiyashi, a cewarsa, hakan ba abu ne da zai faranta wa kowane irin shugaba rai ba.
A wani rubutu ta dandalin Truth Social, Trump ya umarci sashen tsaro na Pentagon da ya tsara yadda za a kai wa Nijeriya hari, kwana ɗaya bayan zargin al’ummar Kiristanci na fuskantar matsi a ƙasar.
Kazalika, Shugaban Amurkan ya jaddada aniyarsa ta kai wa Nijeriya farmaki kan kisa al’ummar bayan bayyanar rahotannin da ke cewa fadar shugaban ƙasa ta nemi a gana tsakanin ɓangarorin biyu domin samun sulhu.
