Ramadan: Rundunar ‘Yan Sandan ta haramta tashe a Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Mamman Dauda, ta hana gudanar da tashe a faɗin jihar a wannan wata na Ramadan.

Hanin na ƙunshe ne a wata sanarwa da Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar tare da raba wa manema labarai a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce Kwamishinan ya bayyana cewa sau da yawa ana amfani da damar tashe wajen aikata miyagun ayyuka a jihar da suka haɗa da sara-suka, harkar daba, ƙwacen waya da sauran laifuka.

Sanarwar ta ce, “Duk wanda jami’an tsaron mu suka cika hannu da shi ko da su, to lallai zai fuskanci hukunci a gaban shari’a.”

Kwamishinan ya ƙara da cewa dokar hana hawan dawakai da buga ‘nockout’ tana nan, don haka babu gudu babu ja da baya wajen hukunta duk wanda a ka kama da aikata laifin haka.

A ƙamarshe, ya ce mutane su yi amfani da damar wannan wata na Ramadan domin gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya, tare da kira ga jama’a da su kasance masu sanar jami’an tsaro muhimman bayanai.

Jami’in ya ce duk lokacin da buƙata ta taso, ana iya tuntuɓar su ya lambobin waya kamar haka: 08032419754, 08123821575, 09029292926.