Sarkin Kano ya naɗa sabbin hakimai, ya ɗaga darajar wasu guda shida

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL, ya sake naɗa wasu sabbin hakimai guda huɗu tare da ɗaga darajar wasu guda shida.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan naɗin, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce an yi naɗin ne bisa cancanta da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Masarautar Kano, Abubakar Balarabe K’Ƙofar Na’isa, ya aike wa manema labarai a yammacin ranar Juma’a.

Waɗanda naɗin ya shafa sun haɗa da Alhaji Nura Sunusi a Matsayin Ɗan Darman Kano da Alhaji Sarki Hamidu Bayero a Matsayin Barayan Kano da Alhaji Sayyadi Muhammad Yola a matsayin Fagacin Kano da kuma Alhaji Bello Idi a Matsayin Kaigaman Kano.

Sai kuma Hakiman da aka ɗaga darajarsu da suka haɗa da Malam Umar Sunusi Bunun Kano inda ya koma Ɗan Makwayyon Kano, Malam Ibrahim Hamza Bayero Ɗan Madamin Kano zuwa Ɗan Ruwatan Kano da Malam Lamido Abubakar Bayero Yariman Kano inda ya zama Bunun Kano.

Sauran su ne, Alhaji Aminu Ahmad Sadiq Zamnan Kano zuwa Ɗan Madanin Kano da Alhaji Magaji Galadima Kachallan Kano zuwa Magayakin Kano da kuma Alhaji Bello Habibu Ɗankadai Fagacin Kano zuwa katikan Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR JP, ya buƙaci hakiman da aka naɗa su zamo jakadu nagari a duk inda suka samu kansu tare da gudanar da aikinsu da gaskiya da amana da sanya tsoron Allah.