Ramadan: Sarkin Kano Sanusi na ci gaba da halartar zaman tafsirin Alƙur’ani

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II PhD CON , ya na halartar zaman karatun Tafsirin Alƙur’ani mai girma da ake gudanarwa a duk shekara a gidan sarkin Kano.

Zaman tafsirin, wanda ya ke samun halartar malamai da al’umma da dama, ya kasance wani ɓangare na shirye-shiryen ibada da ake gudanarwa musamman a irin wannan lokaci domin ƙarfafa ilimin addini da kuma tunatar da al’umma muhimmancin koyarwar Alƙur’ani mai tsarki.

Mahalarta majalisar kan bayyana cewa irin waɗannan zaman tafsiri na taka muhimmiyar rawa wajen ƙara fahimtar addini, da kuma ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin al’ummar musulmi.

An fara gudanar da tafsirin Alƙur’ani a fadar sarkin Kano tun a zamanin sarakunan Kano na farko bayan kafuwar daular Musulunci a yankin, musamman bayan jihadin da Usman Ɗan Fodiyo ya jagoranta a farkon ƙarni na 19.

Wannan jihadi ya kawo sauye-sauye masu yawa a harkokin addini da mulki a Arewacin Najeriya, ciki har da ƙarfafa koyarwar Musulunci da ilimin Alƙur’ani.

Bayan wannan lokaci, sarakunan Kano suka fara ba malamai muhimmanci ta hanyar gayyatarsu zuwa fada domin koyar da tafsirin Alƙur’ani, musamman a watan Ramadan.

A halin da ake ciki yanzu Sheikh Qaribullah Nasir Kabara ne ke jagorantar fassarawa yayin da Gwani Hadi Tahir yake jan baki.

Ana dai gudanar da wannan tafsiri a kullum tun daga ɗaya ga watan Ramadan har zuwa ƙarshensa.

By ukarofi