‘Yan bindiga sun kashe mutane uku da jikkata 11 a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Katsina ta tabbatar da cewa mutane uku sun mutu yayin da wasu 11 suka jikkata lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a garin Jikamshi da ke ƙaramar hukumar Musawa.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar (PPRO), Aliyu Abubakar, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina.

A cewarsa, da misalin ƙarfe 6:05 na yamma, a ranar 10 ga Maris, rundunar ta sami kiran gaggawa a sashen ‘yan sanda dake Musawa inda aka sanar cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, ɗauke da muggan makamai, sun kai hari a ƙauyen Jiƙamshi, ƙaramar hukumar Musawa. “Sun raunata mutane 14 kafin isowar hukumomin tsaro,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa da samun rahoton, wata tawagar haɗin gwiwa ta hukumomin tsaro, ƙarƙashin jagorancin DPO Musawa, ta kai ɗauki cikin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru. Tawagar ta fafata da ‘yan bindigar inda ta samu nasarar daƙile harin.

“An garzaya da waɗanda suka ji rauni zuwa asibiti mafi kusa don neman magani.

“Abin takaici, likita ya tabbatar da mutuwar uku daga cikin waɗanda suka ji rauni, yayin da 11 ke karɓar magani,” in ji shi.

DSP Abubakar ya ƙara da cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda, Bello Shehu, ya yi Allah wadai da harin kuma ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin tare da kama waɗanda suka aikata laifin.

By ukarofi