
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban jam’iyyar PDP a Jihar Zamfara, Dakta Jamil Jibo Magayaki, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar tare da koma wa mai mulki, wato APC.
Magayaki ya bayyana sauya sheƙar tasa ne kwanaki kaɗan da Gwamnan jihar, Dauda Lawal ya koma APC.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, tsohon shugaban PDP na Zamfara ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bisa la’akari da halin siyasar da ake ciki a jihar.
Ya ce, “Ni, Dakta Jamil Jibo Magayaki, shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara, ina sanar da komawata a hukumance zuwa jam’iyyar APC mai mulki.”
