Aminu Alan Waƙa: Bikin naɗin Sarkin Adabi na farko a Daura ya yi armashi 

Spread the love

Daga KHALID IMAM

Waƙoƙin Alan Waƙa tamkar wani madubi ne na duban harshen Hausa da adabi – Mai Martaba Sarkin Daura

Masarautar Daura ta yi cikar kwari sakamakon dandazon dubban masoya da ɗaruruwan ‘yan uwa da abokan arziki da suka halarci naɗin Dakta Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa a matsayin Sarkin Adabin Harshen Hausa na farko a tarihi. Wannan babban al’amari na tarihi a ƙasar Hausa  ya faru ne a Masarautar Daura a daidai lokacin bikin naɗi mai cike da ban ƙaye da armashi, Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Dakta Umar Farouk Umar CON ya cicciɓa darajar Adabi da ma’abota harkokin fasaha ta adabi da naɗin fitaccen mawaƙi kuma marubuci Alan Waƙa wanda sunansa ya daɗe da yin tambari a duniyar Adabin Harshen Hausa a matsayin Sarkin Adabin Harshen Hausa na farko a tarihin masarautar Daura da ma sauran masarautun yakin Arewacin Najeriya da Nijar baki ɗaya.

Naɗin na Dakta Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa wanda aka yi a ranar Asabar, 14 ga watan Fabrairu, 2026 a fadar Masarautar Daura wani babban ginshiƙi ne aka kafa a yankin Arewacin Najeriya da Nijar baki ɗaya, inda aka fi sani da ƙasar Hausa don ƙarfafa gwiwa ga ma’abota harkoki da fasahar adabi a cikin harshen Hausa, harshen da ya mamaye Yammacin Afirka kuma yake ci gaba da naso a wasu sassan duniya.

Tabbas wannan naɗi na fasihin marubuci kuma mawaƙi wanda za a iya kira da cikakken Adibi wani babban lamari ne da wasu marubuta da suka halarci nadin kamar su Ado Ahmad Gidan Dabino MON, Tsohon Shugaban ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya Reshen Jahar Kano kuma Shugaban Kamfanin Gidan Dabino International da kuma Khalid Imam, wato Tsohon Babban Sakataren ƙungiyar Marubutan Arewacin Najeriya kuma Shugaban Kano Literary Space (wato ƙungiyar Marubuta ta Kano) suka ambata da cewa wata hanya ce da ta sake haska irin darajar da Adabin Harshen Hausa yake da shi, kuma lamari ne da zai sake ɗagawa da kambama adabi da Harshen Hausa a duniya.  

Wannan gagarumin bikin ya zo ne a daidai lokacin da Sarkin Daura Dakta Umar Farouk Umar CON ya ke ƙokarin ƙara ƙarfafa martaba da bunƙasa harshen Hausa da adabinsa da kuma al’adun Hausawa ba ma a iya cikin farfajiyar ƙasar Hausa da kewaye ba, har ma a faɗin duniya baki ɗaya.

An gudanar da wannan gagarumin bikin naɗin Sarkin Adabin Harshen Hausa na farkon ne wanda ya yi armashi a ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Daura, Dakta Umar Farouk Umar CON, wanda ya bayyana matukar farin cikinsa da Dakta Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa ya rungumi ɗaga martabar Harshen Hausa da adabi, wanda kuma hakan ne ya sanya ya ga cikakkiyar cancantarsa da wannan sarauta da Masarautar Daura ta ba shi. Sarkin ya bayyana ce, “Tabbas shi a wajensa Alan Waƙa ya wuce matsayin mawaƙi kawai, domin wani babban Jakada ne na Harshen Hausa da adabi da al’adun Hausawa”. 

Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar a daidai lokacin da ya ke daf da miƙawa Alan Waƙa sandar sarautar Sarkin Adabin Harshen Hausa, ya sake bayyana cewa, “Tabbas na gamsu a raina ƙwarai da gaske cewa a bisa irin zalaƙa da gudunmawar da Dakta Alan Waƙa ya ke bayarwa a tsawon shekaru wajen haɓaka Adabin Hausa ta hanyar waƙoƙinsa da rubuce-rubucensa da sauran ayyukan al’adu wanann sarauta ya cancanci a ba shi ita, kuma ina fatan zata ƙara ƙarfafa masa gwiwar cigaba da haska Hausa da taskance gwalagwalan kalmominta a cikin waƙoƙinsa da sauran ayyukan adabinsa.” An yi ta bushe-bushe da kaɗe-kaɗe da waƙe – waƙe bayan da Sarki ya kammala naɗin kuma aka yi wa sabon Sarkin Adabin Harshen Hausa rakiya a bisa dawakai zuwa masauki. 

Washegarin naɗin:

Tun a ranar Juma’a ne 13 ga watan Fabrairu, 2026 ɗaruruwan baƙi mahalarta bikin naɗin Sarkin Adabin Harshen Hausa suka fara tururuwa zuwa garin Daura mai ɗumbin tarihi.

Da isar tawagar angon sarautar Sarkin Adabin Harshen Hausa da tawagarsa wato Dakta Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa sai suka zarce fadar Sarkin Daura don yin gaisuwar al’ada. Sarkin Daura Dakta Umar Farouk Umar CON ne da kansa ya karɓi tawagar ta Alan Waƙa da abokan arziki cikinsu har da Alhaji Abdurrahman Muhammad Mubi  wanda shi ma aka naɗa shi a matsayin Salanken Daura tare da amininsa Alan Waƙa a washegarin rana guda.

Sarkin Daura cike da farin ciki da annashuwa ya karɓi tawagar baƙin da suka isa yi masa gaisuwa da jinjinar bangirma a fadarsa. Mai Martaba Sarkin Daura wanda ya karɓi baƙi a cikin fadarsa wadda ya saba gudanar da muhimman al’amura na masarauta ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya kawo dukkan baƙin cikin tawagar Alan Waƙa garin Daura lafiya. Ziyarar ta gudana cikin tsari, ladabi da girmamawa irin na al’adar Hausawa.

Daren nishaɗi ya yi armashi:

A daren wannan rana ta Juma’a ne Sarkin Daura ya fito tare da sarauniyoyinsa da hakimai fagen zaman nishaɗi da yi wa baƙi maraba. Kafin a fara nishadantarwa da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe da bushe-bushe na al’ada da kuma na zamani cikin harshen Hausa, Mai Martaba Sarkin Daura  ya yaba wa Dakta Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa bisa sadaukarwa da jajircewarsa wajen raya harshen Hausa da al’adun Hausawa, musamman ta fuskar waƙoƙinsa waɗanda da su ya fi shuhura. Sarkin ya nuna cewa waƙoƙin Alan Waƙa tamkar wani madubi ne na duban harshen Hausa da adabi da al’adun Hausawa ban da kuma nishaɗi da tarbiyya da suke koyarwa. Sarkin ya yi wannan cikakken bayani ne a daidai lokacin da ake daf da fara gabatar da nishaɗi a gargajiyance da zamanance a fadarsa.

Masarautar Daura ta shirya gagarumin taron nishaɗi ne wanda ya samu halartar mai gayya mai aiki wato shi kansa Mai Martaba Sarkin Daura da iyalansa da hakiman masarautarsa da masu riƙe da sarautu daga sauran yankunan Arewa, tare da ɗimbin masoya da jama’a daga ciki da wajen garin Daura, duk domin yin maraba da baƙi da nishaɗantarwa, kuma domin a ɗabbaka al’adu irin na dauri.

An yi wannan gagarumin shagalin cikin nishaɗi da annashuwa tare da cin abincin dare na alfarma, a inda kuma fitattun mawaƙa na faɗa da baƙin makaɗan gargajiya daga Kano da mawaƙan zamani daga sassan Arewacin Najeriya suka baje-kolin basirarsu kuma aka yi wa da yawa kyauatar alfarma irin ta sarauta. Wannan bikin daren nishaɗi ya matuƙar ƙayatar da mahalarta taron. Daga cikin mashahuran mawaƙan da suka fi ƙayatar da mahalarta sun haɗa da su zabiya Fati Niger da fasihin makaɗin Kuntugi Alhaji Babangida Kakadawa wanda ya zo tun daga Zamfara garin Daura don kar a yi ba shi. Shi kansa Dakta Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa ba a bar shi a baya ba wajen gabatar da waƙoƙin yabon Sarkin Daura da iyalinsa da kuma Masarautar Daura. 

Mafi yawan mawaƙan da suka cashe sun gabatar da waƙoƙi masu daɗi kuma sun fi rera waƙoƙin yabon Sarkin Daura da iyalinsa da Masarautar Daura, a yayin da wasu kuma kamar Fati Niger ta waƙe Alan Waƙa. Waƙoƙin sun bayyana tarihi, al’ada da kuma nuna muhimmancin adabi a rayuwar al’umma. Dakta Nasiru Wada Khalil ya yi bayani mai janhakali game da matsayin Masarautar Daura a ƙasar Hausa da irin gudunmawar ta a fagen tarihi da a wajen bunƙasa harshen Hausa da al’adun Hausawa a ciki da wajen ƙasar Hausa. Tabbas taron nishaɗin ya kasance wata dama ta haɗa kan jama’a, tare da nuna alfahari da harshen Hausa da ɗabi’un gargajiya na Masarautar Daura.

Muhimmacin naɗin sarautar Sarkin Adabin Harshen Hausa:

Naɗin Dakta Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa a matsayin Sarkin Adabin Harshen Hausa na farko a Masarautar Daura ya zama mabuɗin wani sabon shafi a duniyar tarihin masarautar Daura da ma yakin Arewacin Najeriya da Nijar ba ki ɗaya. Naɗin ya nuna a bayyane yadda sarakunan gargajiya ke ganin ƙima da darajar mutane masu basira da fasaha ba tun yau ba a matsayin wasu dirakun taskance tarihi da tallata harshe da al’ada. Tabbas naɗin na Alan Waƙa wata babbar dama ce  muhimmiya adabi ya samu da muka ma’abota adabi domin cigaba da taka muhimmiyar rawa wajen karewa da cigaba da kuma ɗaga darajar al’adu da harshen Hausa da adabi a aikace.

Ma’abota hankali da hangen nesa a wajen taron sun bayyana cewa wannan mataki na samar da sarautar Sarkin Adabin Harshen Hausa zai ƙara ƙarfafa gwiwar matasa wajen rungumar adabi, waƙa da rubuce-rubuce a harshen Hausa. Haka kuma, zai zama wata hanya ta tabbatar da cewa adabin Hausa ya ci gaba da bunƙasa tare da samun cikakkiyar kulawa daga hukumomin gwamnati da sarakunan gargajiya.

An gudanar da liyafar alfarma a Kano

A daren Asabar bayan dawowa daga garin Daura ne sai masoya da ‘yan uwa da kuma abokan arziki suka halarci wata liyafar alfarma da aka gudanar a sabon ɗakin taro na zamani mai suna Kano City Mall da ke a unguwar Mandawari. Taron ya sami halartar manyan jigajigan masu riƙe da sarautu da tajiran ‘yan kasuwa da masana daga Kano da Zariya da Adamawa da Lafia da sauran sassa da garuruwan Arewacin Najeriya. Haka kuma matasa da mashahuran mawaƙa sun bajekolin basirarsu kuma an yi musu godiya da kyautukan suturu da filaye da kujerun Hajji da kuma kuɗi. Mahalartan wannan walima sun ci sun sha an yi hani’an a wannan dare. An gabatar da takaitaccen tarihin Dakta Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa da kuma na abokinsa Alhaji Abdurrahman Muhammad Mubi wato wanda shi ma aka naɗa shi Salanken ƙasar Hausa.

Manyan masu riƙe da sarautu ciki har da Sarkin Waƙar ƙasar Hausa Alhaji Dauda Kahutu Rarara na daga cikin waɗanda suka halarci wannan walima wato cin abinci na masu alfarma. Da yawa sun taya Dakta Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa murna tare da yi masa addu’o’i na fatan alheri da kuma neman Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin wannan sarauta cikin adalci da hikima da ƙara ɗaukaka adabin Hausa a idon duniya.

Babu ko tantama wannan gagarumin biki ya kasance abin kafa sabon tarihi wanda zai daɗe ana tunawa da shi a Masarautar Daura da kafatanin Arewacin Najeriya da ma duniya baki ɗaya. Naɗin Sarkin Adabin Harshen Hausa na farko ba kawai karramawa ba ce ga mutum guda, tabbas wata alama ce ta girmamawa ga ma’abota adabi baki ɗaya da kuma shi uwa uba harshen Hausa da al’adunsa, wanda adabi ke zame masu madubi.

By ukarofi