Shi’ah ta magantu kan zargin farmakar Amurkawa, ta sanya ranar gangami a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da aka sani da Shi’ah ta ƙaryata zarge-zargen cewa ta shirya kai farmaki akan Amurkawa ko cibiyoyinsu da ke Nijeriya, tana mai cewa ayyukanta suna nan cikin lumana kuma a dokance.

Haka kuma, ta ce ta zaɓi Juma’a, a matsayin ranar Quds da za ta yi gangaminta da kuma jimamin mutuwar jagoran addinin ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Hakan na zuwa ne bayan da ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar da saƙon ankararwa ga Amurkawa kan yiwuwar ‘yan ta’adda ka iya kai hari akan ofisoshin Amurka na harkokin difulomasiyya da makarantu masu alaƙa da ƙasar.

Da yake ganawa da manema labarai a Abuja, Shugaban IMN Resource Forum, Farfesa Abdullah Ɗanladi, ya yi watsi da zargin cewa kungiyar ko mambobinta na shirin kai hare-hare, yana mai jaddada cewa “ƙungiyar ba ta taɓa shiga cikin aikata tarzoma ba”.

A cewarsa, “A tarihin Islamic Movement in Nigeria, wanda aka fara a 1977, ba mu taɓa farmakar kowa ba ko bayar da umarnin a kai wa wani hari.”

Ya kuma ƙalubalanci dalilin da ya sa ofishin jakadancin ya fitar da saƙon ankararwa a madadin kai ƙorafinsa ga hukumomin tsaron Nijeriya.

By Babaji