Daga BELLO A. BABAJI
Yayin da ake bikin tunawa da sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki, manyan jami’an gwamnati da dama ne suka halarci taron a filin taro na Eagles Square dake Abuja, a ranar 15 ga watan Junairu.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, shi ne wanda ya jagoranci sauran manyan jami’an gwamnati don sara wa sojojin da iyalansu bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wajen bai wa Nijeriya da al’ummarta tsaro.
Cikin waɗanda suka halarci taron akwai shugabancin Majalisun Dattawa da Wakilai, shugabannin sojoji, Sufeton ƴan sanda da kuma Alƙalin Alƙalan Nijeriya.
Sauran su haɗa da ministoci, manyan jami’an gwamnati, manyan jami’an sojoji, jami’an difulomasiyya, zaurawan da sojojin suka bari da matan jami’an sojoji.
Acikin wata sanarwa, Majalisar Dattawa ta yaba wa sadaukarwar sojojin da kuma na takwarorinsu da ke cigaba da ƙoƙarin bada kariya ga ƙasar gami da tabbatar da zaman lafiya.