Rashin adalci ne babban ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta, inji Akpabio

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana rashin adalci a matsayin babban ƙalubalen da Nijeriya ke fama da ita.

Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom a yayin addu’ar nuna farin cikin na ɗaga darajar mai shari’a Festus Ntong, zuwa kotun ɗaukaka ƙara bayan bayan shafe tsawon shekaru yana hidimta wa jihar ta Akwa-Ibom.

A cewar sanarwar da mai taimaka wa sanatan na musamman kan yaɗa labarai, Akpabio ya ɗora alhakin matsalar tsaron da Nijeriya ke fama da shi ne kan rashin adalci inda ya ce ba ƙasar da za ta zauna lafiya matuƙar akwai rashin adalci.

“Babbar matsalar Nijeriya ita ce rashin adalci. Duk inda ba adalci, ba za a samu zaman lafiya ba. Ina addu’ar ubangiji ya cigaba da riƙo da hannun alƙalanmu wajen tabbatar da adalci a Najeriya da ma duniya bakiɗaya,” inji shi.

Akpabio ya buƙaci alƙalai da su yi amfani da ofisoshinsu wajen wajen tabbatar da adalci ga wanda aka zalunta.

Sannan ya bayyna mista Ntong a matsayin jarumi wanda ya yi zama na daban cikin abokansa alƙalai tare da roƙonsa kan ya cigaba da riƙo da waɗannan kyawawan abubuwa.

Akpabio ya ce Ubangiji ya amsa masa addu’arsa ta hanyar ɗaga darajar mista zuwa kotun ɗaukaka ƙara inda ya ce, “ina cikin damuwa saboda tun bayan rasuwar mai shari’a Udo Udoma ya ajiye aiki daga kotun ƙoli, na damu kan cewa bayan rasuwarsa zai zama ba wani ɗan asalin jihar Akwa Ibom da ke babbar kotun duk da tarin zaƙaƙurai da muke da su a fannin shari’a.”

“Don haka nai addu’ar ubangiji ya sa bayan ajiye mulkina a matsayin gwamna, ya zamana an samu wani ɗan jihar da zai kai ga wannan matsayi na shiga cikin sahun alƙalan kotun ƙoli, sai kuma ubangiji ya amsa min addu’ata ta hnayar ɗaga darajar mai shari’a Inyang Okoro zuwa kotun ƙoli.”

“Mai shari’a Ntong, ba kai ne na ƙarshe ba. Za a samu wasu da dama da z su biyo bayanka domin jihar nan ta cigaba da ba da gudunmowa wajen wanzar da adalci a Najeriya.”

A cikin jawabinsa, mista Ntong ya nuna jin daɗinsa ga masu yi masa fatan alkhairi da suka samu damar halartar taron wanda ya ce ƙarfin guiwar da suke ba shi ce ta sa yake cigaba da gudanar da aiki al’ummar Nijeriya.

By ukarofi