Rashin aikin yi ga matasan Nijeriya babban haɗari ne — Obasanjo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan yadda matasa ke tashe-tashen hankula sakamakon rashin aikin yi, inda ya yi fargabar cewa Nijeriya na zaune ne a kan abin fashewa.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Financial Times wanda gidan Talabijin na Channels ya bibiya.

“Matasanmu suna cikin tashin hankali. Kuma suna cikin tashin hankali ne saboda ba su da fasaha. Ba su da ƙarfi. Ba su da aikin yi. Dukanmu muna zaune a kan wani abu da zai iya fashewa. Kuma addu’ata ita ce mu yi abin da ya dace kafin lokaci ya kure,” ya yi gargaɗin.

Kalaman na Obasanjo na zuwa yayin da ake zanga-zangar #Endbadgoɓnance da ke gudana a duk faɗin ƙasar da matasa suka yi kan yunwa da ƙuncin rayuwa a ƙasar.

Tun a ranar 1 ga watan Agusta ne dai matasa a faɗin ƙasar suka fara zanga-zanga.

Da yake ƙarin haske, Obasanjo ya ce da tattalin arzikin Nijeriya zai yi kyau matuƙa idan ba a dogara ga samar da ɗanyen mai kawai ba.

Ya bayyana dogaro da ɗanyen man da ƙasar ke yi a matsayin “mummunan kuskure”. “Na yi imani mun tafka babban kuskure ta hanyar sanya ƙwayayenmu duka a cikin kwando ɗaya ta hanyar dogaro da mai. Muna da kaya masu muhimmanci, iskar gas, amma ba ma duban su,” in ji shi.

Akwai kuma gazawar Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Kamfanonin Mai na duniya, da sauran kamfanonin mai na kasa wajen inganta hako mai domin biyan buƙatun ƙasar.

Obasanjo ya ce Nijeriya za ta iya zuba jari sosai a harkar noma mai makon kawai ɗanyen mai.

“Amma mun yi watsi da harkar noma wacce za ta iya iya zama jigon jarinmu.”

By ukarofi