Rashin haɗin kai ne ya mayar da masu Yabon Manzon Allah baya – Bashir Ɗandago

“17 daga cikin ‘ya’yana ne suka zama mawaƙan yabo”
“Asalin majalisi ba da mandiri ake yin sa ba”

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

A daidai lokacin da harkar Yabon Manzon Allah S A W ta shiga wani yanayi na gasa da neman suna, uwa uba kuma da rashin haɗin kai a tsakanin Sha’iran wanda hakan ya jawo musu koma baya a cikin harkar ta su, wannan ta sa muka nemi jin ta bakin tsohon mawaƙin Yabon Manzon Allah S A W domin ya bayyana mana yadda harkar Yabon Manzon Allah S A W ta samo asalin tun kafuwar ta a cikin garin kano da ma yadda ta yaɗu zuwa wasu jihohi har ma da ƙasashen waje. Don haka, sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar da kan ka ga masu karatunmu.
BASHIR ƊANDAGO: To Alhamdulillahi, ni dai kamar yadda aka sani suna na Bashir Abubakar Ɗandago wanda aka fi sani da Bashir Ɗandago mawaƙin Yabon Manzon Allah S A W, na dauri kuma har zuwa wannan lokacin. An haife ni a Unguwar Ɗandago a wani gida da a ke kira gidan Rafi, babban gida ne wanda a yanzu akwai mutane sama da dubu a cikin sa, kuma duk kusan zuri’ar mutum ɗaya ne, kuma an haife Ni a shekara ta 1965, na yi karatuna a nan firamare ta Ɗandago, na kuma gama, na tafi kwalejin koyon kasuwanci ta Aminu Kano. Bayan na kammala na je don na yi karatun share fagen shiga Jami’a, to amma daga nan sai na tafi na yi Diploma, a ɓangaren arabiyya kuma na yi karatun Kur’ani a wajen Malam Tayo dake Unguwar ‘Yar maishinkafi, a ɓangaren Littafi kuma na zauna a gaban Sheikh Nasiru Kabara na karanta littattafai da dama a wajen sa, da kuma Malamina, Malam Ɗanyaro. kuma ɓangaren iyali a yanzu haka Ina da mata 3 da yara 25 masu rai, biyar Allah ya yi musu rasuwa, ka ga na haifi 30 kenan, kuma Ina godiya ga Allah a cikin 25 ɗin nan 17 masu Yabon Manzon Allah S A W ne.

Duniya ta san ka a matsayin mawaƙin Yabon Manzon Allah S A W tun da ka taso. Ko za ka faɗa mana yadda ka fara?
Lallai kam harkokin Yabon Manzon Allah S A W Ƙungiyar Ƙussha’u ce ta rene ni, don a cikin ta na tashi tun da yarinta ta Ina daga cikin waɗanda suka ƙarfafa ta har zuwa tsawon lokaci a yanzu zai kai shekaru 40 kenan, saboda haka da ni aka kafa ta tun kafin a fara saka lasifika a wajen Majalisi, tun ana saka fitila a haska a zo a karanta waƙoƙi a rubuce ma har ta kai an zo ana yin ta a bainar jama’a.

Ita Ƙussha’u ka samu kan ka ne a cikin ta ko da ku aka kafa ta?
To gaskiya ba da ni aka kafa ta ba, don na shigeta ne a matsayina na Sha’iri, domin ni asalina mawaƙin Hallara ne tun da a gidan Ƙadiyya na tashi, kuma shi gida ne da ya shafi waƙoƙi na magabata. Hasali ma ni mai jan Hallara ne, Ina jan waƙoƙin Mandiri da kuma na Hallara, to daga nan na samu gogewa kafin na shigo Usshaqu, shi ya sa da na shigo na same su suna yi, sai ya zama na samu ƙwarewa.

To ya yanayin waƙoƙin yake a wancan lokacin da kuma yadda a ke tafiyar da su?
To a wancan lokacin ita Usshaƙu uwa ce, ko’ina aka shiga dattawa da manyan mutane a ke zuwa wajen su ana kafa Majalisi, ma’ana shehunan mu irin su Sheikh Yusif Ali a kan je wajen su a zauna a yi. Allah ya jiƙan jagora Malam Tijjani Tukur Yola, a matsayin sa na uba na wannan ƙungiyar ana zuwa gidan sa a zauna a yi, har gidan Ƙadiyya muna zuwa gaban Malam Nasiru Kabara, ana zuwa saboda haka babu irin gudunmmowar da Malam Nasiru Kabara bai ba wannan ƙungiyar ba. Har ma ɗaukar ƙungiyar yake yi zuwa wasu garuruwa don tallata ta, saboda haka mun sha wannan gwagwarmayar ta yaɗa ta.

Idan na fahimce ka a baya ana gudanar da Majalisi ne a gidan shehunai.
E haka ne, muna zuwa gidan shehunan mu ne, sai daga baya aka tsara kalanda na sati guda ko na wata kamar a tsara ranar kaza ga watan kaza muna unguwa kaza, saboda haka sai mutanen unguwar su ci gaba da shiri ba sai da biki ko suna ba, sai kuma daga baya aka fara saka lasifika don a ji abin sosai har aka fara gayyata zuwa Mauldi ko suna.

Kenan dai ba da Mandiri kuke yin Majalisin ba?
Ai daman shi Mandiri daga baya ya zo duk zaman Usshaƙu da muka yi ba da Mandiri muka yi ba, kuma ba ma a tsaye muke yi ba, idan ka ga mutane a tsaye to ‘yan harraƙawa ne, amma su mawaƙan a zaune a ke an yi da’ira in ya zo kan ka sai ka shigo tsakiya a ba ka lasifika ka yi waƙa, in da gyara a ba ka shawara a ce ka bar kaza waje kaza bai yi daidai ba, saboda haka waƙoƙin a ke yi tsuran su babu maganar kiɗa.
Farkon saka kiɗa ya samo asali ne daga wata ƙungiya ta Ahbabu, ita ce ta fara saka Mandiri a cikin waƙar Yabon Manzon Allah S A W, kuma ita ce ƙungiya ta biyu da aka kafa bayan Usshaƙu sai ita, domin abin ya fara yawa a lokacin mutane sun yi yawa, to sai Marigayi Sidi Musa ya nemi izini a je a buɗe masa ƙungiyar Ahbabu. kuma Alhamdulillahi, Ina ɗaya daga cikin mutanen da suka bayar da gudunmawar su a cikin ta, to sun fara babu Mandiri daga baya sai suka yanke shawara suka fara saka Mandiri a harkar Majalisi. Amma ita ƙungiyar Usshaƙu har yanzu ba ta saka Mandiri, kuma daga lokacin da aka fara saka Mandiri daga nan aka fara yaye wasu ƙungiyoyin, aka yi Jama’atul Ahbabu wadda Malam Magaji ‘Yantandu shi ne shugaba, Marigayi Rabiu Usman Baba a matsayin mataimakin shugaba, aka zo aka yi Jindullahi wanda Ali Siffa Marigayi ya zama shugaban ta da sauran ƙungiyoyin waɗanda duk Sha’iran da kake ji wane da wane idan ba ka fito daga cikin ƙungiyoyin nan ba, to wanda ya koyar da kai daga cikin su ya fito.

Ya ya tafiyar Majalisi yake bayan ƙungiyoyi sun ƙaru?
To ƙungiyoyi sun ƙaru, kuma Mandiri ya karɓu ana yi a can ana yi a nan, to sai ya zama cewa an fara tunanin yayewa, wato ma’ana daga ɓangaren Jama’atu sai su Bashir Ɗan Musa suka samu damar buɗe Jindu. To daga nan kuma sai ya zama Bashir Ɗan Musa shi ya fara zama kai kadai gayya, wato shi kaɗai ya tafi Majalisi ko wajen biki ko suna don haka duk wanda zai ce ya mallaki lasifika, ya haɗa kayan sa yana Majalisi to a wajen Bashir Ɗan Musa ya gani, domin shi ne ya fara yi a cikin Sha’irai, amma da ƙungiya a ke yi a tafi shi ne ya fara warewa yana tafiya da yaransa. To daga nan ni Bashir Ɗandago Ina daga cikin wanda na biyo bayan sa sai na yanke shawarar ni ma na kama gaba na, to daga nan sai kowa ya fara yin na sa da jama’ar sa. Misalin kamar Kabiru Dogarai ai akwai ƙungiyar su ta Diya’u, amma daga baya wasu matsalolin suka sa ya zo ya kama gaban sa kuma ya ɗore a haka har yanzu, ni har yanzu idan ana Majalisi na Usshaƙu Ina zuwa na zauna saboda ni ɗanta ne, amma dai na kama gaban kaina Ina zuwa ko’ina a duniya Ina Majalisi.

To da yake rayuwa ta tafi a yanzu wanne irin shiri ka yi wa rayuwar ka a matsayin ka na Sha’iri?
To Alhamdulillahi, ni ba ni na yi wa kaina shiri ba, na san Allah ya riga ya yi mini, don Allah shi ya so tsara mini rayuwa ta a gidana, don kamar yadda na faɗa maka ina da Sha’irai guda 17 a yanzu a gidana maza da mata, kuma ni kaɗai Allah ya yi mini baiwa ina da yaro yana ɗan shekaru 3 ya fara waƙar Yabon Manzon Allah a yanzu shekarun 7 kuma ya zagaya duniya an san shi, saboda haka wannan ginin da aka fara ba tsari na ba ne na Allah ne, haka ya tsara rayuwar Bashir Ɗandago a harkar Yabon Manzon Allah ba za ta ƙare ba, don haka ma za ka ji ana cewa da gidana Ahlin gidan Faɗima a Siga biyu ta farko ɓoyayyiya wadda ba sai na faɗa maka ita ba, don yaran Ahlin gidan Faɗima ne ta jini, kuma gidana sai aka rubuta masa gidan Fatimatu.
To wannan shi ya sanyya ko’ina idan aka ga yaron gudana sai a ce na gidan Faɗimatu ne saboda haka wannan gidan ka ga zai kafu, ina da rai ko ba ni da rai.

Ya kake kallon yadda harkar Yabon Manzon Allah take kasancewa a wannan lokacin?
Alhamdulillahi sai dai mu ce mun godewa Allah. Farko dai an samu matsaloli kala-kala. Matsalolin da muka samu su ne, bayan mun samu masu kula da mu tsakanin su da Allah, amma mun samu tasgaro a tsakanin mu da su. Misali za ka samu masu kula da mu irin Alhaji Aminu Ahmad mai turare, Makaman Gado da Mason Kano da irin su Alhaji Sabi’u Baƙo, Yahaya Zakarin mai ƙusa, Alhaji Ahmad Ɗanyaro da sauran masu kuɗi da suka rinƙa yi wa mawaƙan Yabon Manzon Allah hidima iya ƙarfin su da ba su kujerar Makka. To amma sai aka samu matsala mu kan mu da ya kamata a ce mun riƙe abin hannu biyu sai ba mu yi ba, don haka su da su ke yi mana hidimar sai ya zamana an shiga inuwar su an yi kashi, sai ya zama sun ja da baya saboda ana samun rashin gaskiya a cikin mu, saboda haka an samu wannan matsala sai ya zama an shiga wani hali da a ke ciki yanzu in aka ce wani mai kuɗi ya fito yana son Yabon Manzon Allah, to sai a samu wasu sun je a guje sun je wajen sa sun tsaya, idan suka kewaye shi, to ba za su bari wani ya je kusa da shi ba, sai wanda su ke so, kuma idan suka tarar da wani a wajen, to sai sun yi masa hayaƙi ya fita, don haka su suke so su tsara yadda suke so, don haka harkar Yabon Manzon Allah a yanzu, sai dai a ce innalillahi wa inna ilaihi raji’una, ba a ganin girman masu girma daga yau ka tashi har kana ganin an ji ka sai ka rinƙa kallon waɗanda ka tarar ɗin banza ne, yanzu kai a ke yi kana sama da su, bayan har ka gama ba za ka samu irin matsayin da ɗaukakar da suka samu ba.

A baya mun manta ba mu yi maganar yadda aka shigo da Mandiri ba kamar yadda ka ce farko ba a yi da shi.
To wanda ya shigo da Mandiri dai Sidi Musa ne, amma shigar da Fiyano abu ne wanda yake ta fuska uku, farko dai a ɗauki Fiyano a je a buga shi a wajen Majalisi, ni Bashir Ɗandago, ni na fara yi don waɗanda suka san lokacin za su tuna wata guntuwa ce nake tafiya da ita har gidan biki da hannu na nake buga ta, saboda haka da aka shiga ‘studio’ za a fara waqa a yaɗa ta, nan ma ina cikin wanda na fara, amma ba ta Yabon Manzon Allah ba, na yi wa Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ne kuma ta yi tasiri wadda har sarkin ma ya ji daɗin ta. Amma a shiga ‘Studio’ a buga waƙa a yaɗa ta, Rabiu Usman Baba shi ne ya fara, waƙoƙin sa irin su ‘Rabbi Rabbi’ da sauran su, don ya tava samu na ya ce, ya samu ƙalubale wajen yin waqa da Fiyano ta Yabon Manzon Allah. Amma Ina mamaki kai sarki ma ka yi wa, amma ba na ganin ka samu ƙalubale kamar yadda ka samu.
Sai na ce da shi gaskiya ne ni idan na yi abu babu ruwana kawar da kai nake yi don haka kai ma ka kauda kan ka ka yi abin da za ka yi da haka za ka samu nasara, kuma Alhamdulillahi don sai da ya zama duk wata jiha sai da ya je ya yi Majalisi da Fiyano, har ya bar duniya kuma da Fiyano yake amfani kuma har a na ƙasa da shi za a ci gaba da koyi idan an samu lada to yana da kamasho.

Gwamnati ta ba ku damar ku gyara, amma rashin haɗin kai ya hana ku yin hakan. Ko ta ina za ku warware waɗanan matsalolin?
Ai tun da Hukumar Tace Finafinai ta kasa haɗa kan Sha’irai ai Ina ganin a jira a gani daga Allah kawai, domin ta shiga ta yi wa kowa katin shaida, to amma matsalar a jagoranci take, idan aka ɗakko wani aka ɗora shi sai ya saka son rai a ciki, saboda haka shi kuma shugaban hukumar ya ɗauki abin da zafi, sai ya zama ƙarshe abin ya yi shiru, don haka tun da Hukumar Tace Finafinai ta gaza to fa kawai sai dai a yi addu’a, don na so a ce matasan nan sun haɗe kan su, su rabu da mu manyan saboda su za mu bar wa, to amma sai abin ya zama ba haka ba.

Mene ne saƙonka na ƙarshe?
To ni dai nasiha zan yi, abin da nake nufi shi ne, Sha’irai su sani harkar su ta Manzon Allah ce, don haka a rinqa ganin sa a aikace a wajen ku, yadda ku ke faɗar Manzon Allah ya kamata a gani a wajen mu’amular ku, amma ba a gan ku kuna yabo ba a can gefe a gan ku da ‘yan shaye-shaye ko a can a ga wani yana bin mata, don haka Ina kira a gare su, su zama cewa, Manzon Allah suka dosa daga zuciyar su har aikin su.

To Madalla, mun gode.
Ni ma na gode sosai.