Rashin koyar da yara sana’o’i na daga cikin abubuwan da ke gurɓata tarbiyyar matasa — ABM

Spread the love

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano

Alhaji Abubakar Muhammad, wanda aka fi sani da ABM Uba, ya bayyana cewa rashin koyar da yara sana’o’in gargajiya da na zamani na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da gurɓacewar tarbiyyar matasa a yau.

ABM, wanda fitaccen ɗan kasuwa ne a ƙungiyar masu sayar da motocin noma a Arewa, ya ce sana’o’i irin su ɗinki, kafinta, jima, saƙa, ƙira da sauran sana’o’in hannu sun kasance hanyoyin neman halal da iyaye ke amfani da su wajen rufa wa kansu asiri, amma yanzu an yi watsi da koyar da yara waɗannan sana’o’i.

Ya ce idan iyaye da ‘yan uwa suna tafiya da yara zuwa kasuwa ko wuraren sana’a bayan sun dawo daga makaranta, hakan na taimakawa wajen gina tarbiyya da hana su shiga mu’amala da marasa tarbiyya.

Ya yi kira ga iyaye, shugabanni da masu hannu da shuni da su tallafa wa matasa ta hanyar samar musu da damar koyon sana’a, yana mai cewa barin yara babu abin yi bayan makaranta babban kuskure ne.

Haka kuma, ya buƙaci gwamnatin tarayya da na jihohi su ƙara tallafa wa manoma da taki, iri da kayan aikin noma na zamani, yana mai cewa fiye da kashi 60 cikin 100 na ‘yan Nijeriya sun dogara da noma a matsayin hanyar samun abin rayuwa.

A ƙarshe, ABM ya ce ya kamata gwamnati ta tabbatar cewa duk wani tallafin noma ya isa ga waɗanda suka cancanta, tare da amfani da shugabannin al’umma kamar masu unguwanni, dagatai, hakimai, sarakuna, limamai da shugabannin ƙungiyoyi wajen rabon tallafin.

Ya kuma yi kira ga gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro, yayin da ya buƙaci al’umma su ci gaba da yin addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.

By ukarofi

Leave a Reply