Rashin samar da wadatattun kayan shan ruwa ya tunzura kwamashina a Jigawa

Spread the love

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Kwamashinan ayyuka na musamman, Alh Auwalu Danladi Sankara ya nuna damuwarsa kan yadda ake yi wa gwamnatin jihar zagon kasa ta fuskar ciyar da al’umma abinci a lokacin buɗe baki a mazabun da gwamnatin ta ware guda 634 albarkacin wata Ramadan.

Kamar yadda ya wallafa shafinsa na Facebook, Sankara ya ce “Mun samu labari da rahotanni na wasu cibiyoyi da ke samar da abincin shan ruwa (buɗa baki) da ba su cika ba a lokacin shirin ciyarwa na watan Ramadan da gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya. A ƙasa akwai cibiyoyin da dillalan da suke kai abincin da bai cika ba”

Ya yi misalai da ƙananan hukumomi kamar haka; A ƙaramar Hukumar Garki akwai;

  1. Garki – B: ansamesu da Rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara ayi
    Sai karamar Hukumar GUMEL ,a Gumel
  2. Gumel – Cibiya 1: Suma ansamesu da Rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara ayi

Haka zalika a karamar Hukumar Guri
A kauyan i – MUSARI a amwati mai lamba 001: ansamesu da laifin Rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara ayi

Haka a ƙauyen – ADIYANI a Amwati Mai lamba 001: Suma an kama su da laifin rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara a bai wa jama’ar.

A Amwati Mai lamba ta 002, bincike ya nuna akwai rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara abaiwa Jama a.

Kazalika, a ƙaramar hukumar Gwiwa a ƙauyen Shafe da Karshi: Ƙunshin da bai cika ba Ake rabawa Jama,a

Bugu da ƙari, a Gwiwa cikin gari da mazabar – Zauma da Sainawa: Kunshin da bai cika ba aka rabawa Jama a sabanin yadda aka tsaara za ayi .

A Hadejia, a Unguwar Kasuwar Kudu (CENTRE A): Shinkafa da ƙosai 280 aka raba wa masu azumi.

Bayanai sun nuna cewa, a ƙaramar Hukumar Jahun a ƙauyan Kale (kale cikin gari): an samu Rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara

Haka kuma a ƙauyen bura-buri: Rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara

Binciken ya gano cewa, a Malam Madori a mazaɓar Arki, kunu kawai aka raba wa mutane da ƙosai 100.

A. Roni da Amaryawa (Center A): shinkafa fakiti 107 kawai aka rabawa mutane
Haka a Roni – Amaryawa (Center A): Kosai 170, Shinkafa 100.dauri Dari aka Raba

A ƙaramar hukumar ta Roni a. Roni – Fara – Kagadama: Shinkafa da Kedar Kunu 208, Kunu 207 aka rabawa mutane

. Kuma mazabar – Kwaita: – a Roni an Sami Rashin samar da isasshen abinci kamar yadda aka tsara.

A kwanan huguma .a ƙaramar humar Dutse, Masallachin Malam Zakariyya kandi.da unguwar Zai Junction, – Asabe Muhammad nanma ansami karancin abincin BA ayishi kamar yadda akece ayiba

Kwanar Huguma a Dutse, Gida Dubu Masallacin Malam Ismail Ringim – Ruƙayya M. Abdullahi.

Kwamashinan a cikin fushi ya ce, “a matsayina na Kwamishinan Ayyuka na Musamman da ke da alhakin kula da wannan shirin, ina so in yi gargaɗi ga duk wani dillali da masu ruwa da tsaki a wannan harkar na abincin ciyarwa na buɗa baki.”

Ya hori waɗanda gargadin ya shafa dasu dauki gargaɗi ya zama sanarwa ta ƙarshe ga duk wanda ke da alhakin shirya abinci, duk wanda aka samu da bada ƙunshin da bai cika ba ko kuma aka same shi da hannu cikin kowane nau’i na rashin bin ƙa’ida ko amaja, to za a hukunta shi a ƙarƙashin doka.

By Babaji