
Daga BELLO A. BABAJI
Kwamitin Kula da Ƙwarewa da bin dokoki da sauraron ƙorafi na Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar na cin zarafi da rashin mutunta aiki akan Shugaban majalisar, Godswill Akpabio.
A ranar Laraba ne kwamitin ya bayyana cewa, akwai saɓa wa aiki acikin al’amarin, inda Shugabansa, Neda Imasuen ya ce Natasha ce wadda ta sanya hannu akan takardar ƙorafin a madadin bai wa wani daban, kamar yadda dokar majalisar ta ayyana.
Haka kuma ya ce, maganganun da ta yi a takardar ƙorafin, tuni aka miƙa su kotu gabannin a gabatar wa majalisar, wanda hakan ya sa batun ya fi ƙarfin majalisar ta ji da shi.
Sannan duk da kwamitin ya shirya batun zaman binciken a ranar Laraba, Natasha ba ta halarci zaman ba.
Da farko, Natasha ta miƙa wa majalisar takardar ƙorafin ne akan Shugaban majalisar, wanda daga baya ya musanta batun zargin nata akansa da yin watsi da su a matsayin ƙarairayi.
