Rashin tsaro ne ke kassara mu, inji matan FOMWAN a Bauchi

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Ƙungiyar Mata Musulmi ta Nijeriya (FOMWAN) reshen jihar Bauchi ta bayyana damuwar ta dangane da matsalar rashin tsaro da yake addabar ɗaukacin mata a ƙasar nan, tana mai cewar, shekaru biyu da suka gabata, ƙalubalen ta kai ɗalibai mata bango a makarantun boko da na Islamiyya.

Wannan ƙalubale, a cewar ƙungiyar, tana buƙatar gwamnatoci a dukkan matakan mulki, su bijiro da wasu tsare-tsare na ilmantar wa da zai bai wa miliyoyin yara damar samun ilimi ba tare da wani barazanar rashin tsaro ba.

Shugabar ƙungiyar ta jihar Bauchi, Amirah A’ishatu Ibrahim Kilishi, ita ce ta yi furucin wannan ƙalubale a ranar Asabar da ta gabata a taron ta na shekara-shekara na 36, na tsawon kwanaki biyu kan Maudu’ih Da’awa, da aka gudanar a ɗakin taro na Babban Masallacin Bauchi.

Hajiya A’ishatu Kilishi ta ce ya zama wajibi a samar wa ɓangaren ilimi tallafi ko gudunmawa domin a rage yawan ɗalibai da suke guje wa makarantu, musamman ‘ya’ya mata saboda rashin tsaro.

“Har wa yau, wani lokaci ne kuma daya kamata al’ummar Musulmi su yi bibiyar rashin halartar mata a wajen tarurruka da suka jiɓanci cigaban al’umma a matsayin su na jigon al’umma cikin wannan yanayi mai cike da tarin ƙalubaloli.”

Kamar yadda ta ce, wajibi ne mata su yi kyakkyawan shiri na tunkarar wannan duniya mai cike da tarin fasahar zamani da suka karaɗa dukkan lamuran rayuwa, haɗi da rawar da suke takawa ta rainon  al’ummar gobe.

Kilishi ta kuma fahimci cewar, mata suna buƙatar ingantaccen ilimin Islama, ilimi na yadda za su yi asmfani da fasahar zamani domin taka rawar da suke yi na ilimantar da yara ƙanana da sauran al’amuran rayuwa.

Ta kuma zayyana ƙalubale na biyu wanda ya jiɓanci jagoranci wa mata da yara a cikin wannan yanayi na talauci da ƙasar take ciki, haɗi da faɗuwar darajar naira, tsadar kayayyakin abinci da kuma tauye hanyoyin rayuwa sakamakon cutar Korona da ta addabi duniya.

Amirah ta FOMWAN a Bauchi ta kuma jaddada buƙatar gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa na samun wadatar abinci wa kowa da kowa ta hanyar farfaɗo da darajar naira da kuma daƙile hauhawar farashin abinci ya zuwa gwargwadon aljihun talaka.

Dangane da haka, Kilishi sai ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta inganta shirin ta na tallafi wa tattalin arzikin mata yadda zai karaɗe lungu-lungu da saƙo-saƙo na ƙasar nan, musamman ya zuwa mata masu raunin tattalin arziki, ko ‘yan ya Allah ka wadata mu.

Ƙungiyar ta FOMWAN ta kuma ji takaicin yadda ake cin mutuncin mata da ‘yan mata a matsayin su na uwayen ƙasa, tana mai cewar, wannan babbar barazana ce ga rayuwar mace da martabar da Allah ya yi wa mata wanda addinin Islama ya koyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *