Rasuwar Aminu Bono ta haifar da wagegen giɓi a Kannywood – Ganduje

Spread the love

Da BASHIR ISAH

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rasuwar Darakta a Kannywood, Aminu Surajo Bono, a matsayin babban rashi ga masa’antar fina-finai.

Ganduje ya bayyana kaduwarsa game da rasuwar marigayin, inda ya ce mutuwar tasa ta zo a daidai lokacin da aka fi bukatar marigayin.

Sanarwar da Sakataren Yada Labarai ga Ganduje, Edwin Olofu, ya sanya wa hannu wadda aka kuma aka raba wa manema labarai a ranar Talata ta ce, “Bono ya yi wa takwarorinsa zarra wajen bada hima da kuma yada al’adun Hausa/Fulani”.

Sanarwar ta kara da cewa, a halin rayuwarsa, marigayin ya bada gagarumar gudunmawa wajen cigaban masana’antar Kannywood.

“Ina so in yi amfani da wannan lokaci wajen nuna alhini ga iyalan marigayin da ma Kannywood baki daya dangane da rasuwar hazikin Darakta a masana’antar, Aminu Surajo Bono,” in ji Ganduje.

Ganduje ya kara da cewa salon rayuwar marigayin ya kyautata mutuncin Kannywood a idon wadanda ke yi wa masana’antar wani kallo.

“Dole ne in yarda da cewa rasuwar Aminu Surajo Bono ta haifar da wagegen gibi a masana’antar fina-finai,” a cewar Ganduje.

A karshe, Ganduje ya yi addu’ar Allah ya bai wa iyalan mamacin da masana’antar Kannywood hakuri da juriyar wannan rashi, kana Ya sa Aljannatul Firdausi ta zamo makomar marigayin.

By Editor