Daga AISHA ASAS
Akwai bambanci sosai tsakanin wadda aka saki da wadda mijin ya mutu – Sa’adatu Kankia
“Ta hanyar gina matanku ne kawai za ku samun tabbacin ‘ya’yanku ba za su tagayyara bayan mutuwarku”
Kamar yadda aka sani, shafin Gimbiya na jaridar Blueprint Manhaja bai tsaya a iya tattaunawa da mata kan rayuwarsu ba. Shafin kan taɓo matsaloli, cigaba da kuma wani abu da ke ciwa mata tuwo a ƙwarya, don tattaunawa da kuma nema masu mafita.
A yau shafin zai yi duba kan halin da mata ke shiga bayan mutuwar mazajensu, wanda ba kasafai ake fahimtar halin da suke shiga ba.
Ita mace rayuwarta gabaɗayanta a ƙarƙashin wani take yin ta. Anan ba wai ina nufin ba ta da ‘yancin yin wani hukunci ga rayuwarta ba, ba kuma ina nufin baiwa ce da ba ta da iko sai yadda aka yi da ita ba. Mace na da ‘yanci da Musulci ya bata da ƙima da kuma daraja, duk da cewa ba kasafai ake faɗar su ba. anan ina zance ne kan yanayin hallita da kuma matsayinmu na ‘yan Arewa ko Hausawa a taƙaice.
A lokacin da aka haifi mace tana ƙarƙashin kulawar iyayenta, daga jarinta zuwa girma har zuwa balaga, wanda daga nan ne ake samun canji wurin zama ga mace, wanda ya danganta daga tsarin iyayen ko kuma lokacin da Allah Ya ayyana ta zama ranar barin ta gidan iyayenta.
Ma’ana, wasu iyayen na da sha’awar barin ‘ya’yansu su yi karatu mai zurfi don haka ‘ya’yansu mata za su zauna har su kammala karatunsu. Yayin da wasu iyayen ke saurin sauke nauyin ‘ya’yansu mata daga kansu ta hanyar aurar da su.
Yayin da haka ta kasance, rayuwarsu da kulawarsu za ta koma hannun mijin da suka aura. Za su yi rayuwa ƙarƙashin kulawarsu da ɗaukar ɗawainiyarsu har izuwa ɗaya cikin biyu; ko dai rabuwar aure ta zo wadda kulawarsu zata yi ribas ta koma ga hannun da ta baro, wato hannun iyayenta. Haka take kasancewa idan mijin ya rasu a lokacin da suke da ƙarancin shekaru ko ba su fita shekarun aure ba.
Mataki na ƙarshe na rayuwar, wato tsufa ta kan yi shi ne ƙarƙashin kulawar ‘ya’yanta maza ko ‘ya’yan ‘yan uwa ko makamatan su.
Da wannan za mu iya cewa, matar bahaushe ba ta saba da tsayuwa da ƙafafunta ba, don haka a duk lokacin da ta rasa majingini rayuwarta ke shiga mawuyacin hali. Anan ba wai ina zancen iya sana’a don dogaro da kai ba. Zancena kan yadda halittar ta take da sabo na kula da ita.
Gabaɗaya rayuwar mace ba a yi ta don ɗaukar ɗawainiya ba ko a Musulunce. Lokacin da take gidan iyayenta aka ce ubanta ya bata ci da shi da sutura. Babu inda aka ce dole sai ta fita ta nema wa kanta, koda kuwa zata tsufa a gidan iyayenta.
Haka idan ta yi aure, waɗannan haƙƙoƙin da suka rataya kan ubanta sun dawo kan mijinta da wasu ƙari na haƙƙin aure.
Idan kuma ta tsufa, aka ce ‘ya’yanta su kula da ita, wanda wajibi ne kansu.
An tambaye wani magabaci, mene ne matsayin magidanci ga iyalinsa? Ya ce, rumfa ce da ke ba su kariya daga ruwa, rana da kuma iska. Yayin da ya zama babu, to sun rasa wannan rumfar, idan ba wani hukunci ba, ruwa da rana za su dinga bugun su, don ba su da abinda zai ba su kariya daga gare su.
Idan muka yi duba da kamalamsa za mu fahimci cewa, kowacce mace da mijinta ya mutu kuka biyu take yi, musamman idan tana da ‘ya’ya da shi.
Anan ba iya matan masu kuɗi ba, har matan masu rufin asiri, koda kuwa a gidan haya suke zaune.
Matan kan shiga mawuyancin hali yayin da suka rasa mazajensu, wanda zai kai ga canza rayuwar tasu bakiɗaya.
Yayin da miji ya mutu ya bar matarsa da ‘ya’yansa, abu na farko da matar za ta iya fuskanta musamman idan tana cikin shekarunta, ma’ana ba ta wuce aure ba shi ne, fargaban a rabata da ‘ya’yanta da sunan ‘yan uwan mijin nata za su riƙe su, ko kuma iyayenta su ne mi hakan don ta tafi ta auri wani.
Wannan hukuncin na iya zama wata barazana ga tarbiyyar ‘ya’yan nata, kasancewar ba kowane ɗan uwa ne zai riƙe ɗan ɗan’uwansa tamkar nasa ba. Wasu ma saboda tsabar rashin tsoron Allah suna karɓar ‘ya’yan ne don hangen ɗan abinda uban ya bar masu gado, da sun ɗan cinye gadon sai su fara ƙorafi, ƙarshe dai su nemi rabuwa da yaran ko kuma wahala ta sa su gudu don neman mafaka.
Sau da yawa duk ni’imar da mace ta samu a gidan sabon mijinta, ta kan tsinci kanta a halin damuwa, tare da shiga tsaka mai wuya, sakamakon halin da ‘ya’yanta suke ciki da kuma zaɓin da sabon mijinta ya bata, na ko zama da shi ko riƙon ‘ya’yanta, a cewarsa ba zai iya riƙe ɗan wani ba.
Ita kuma a kullum tana jin labarin halin da ɗanta yake ciki wanda yake buƙatar kulawarta, saidai dole ta zaɓa tsakanin aurenta da ɗanta.
ƙalubale na biyu kan samu a lokacin da aka gama zaman mutuwar, yayin da aka yi mata hidima ta marmari, wato wannan ya kawo, wannan ya kawo na ɗan lokaci. A lokacin rayuwarta da ta ‘ya’yanta za su san haƙiƙanin ma’anar maraici. Anan za a iya samun sauƙi idan ya kasance tana sana’a tun a baya, don haka ta iya dogaro da kanta, hakan zai sa za su sami sauƙi ta ɓangaren ɗawainiya.
Wannan kuwa wani ƙalubale ne ga matan da kuma mazan. Abinda ya sa na ce dukkansu, saboda kowanne na da gudunmawar da zai iya bayarwa.
Idan zan iya tunawa a kafar Facebook ne na ci karo da wani rubutu na wani bawan Allah da yake janyo hankalin mazaje kan gina matansu, inda ya ce, su gina matansu domin lokacin da suka mutu ba wanda zai iya kula masu da ‘ya’yansu kamar uwar ta su.
Rubutun za mu iya cewa da mazan Arewa ya fi tasiri, domin su ne masu ɗabi’ar ƙin neman na kai ga mace. Wasu na ganin idan ka bar matarka na neman na kanta za ta iya fin ƙarfinka. Wasu kuwa tsabar ƙeta ce kawai, fatansu matansu su zama goro ko abin siyen shi, don haka ko hango ‘yan canji suka yi hannun matan nasu hankalinsu ba ya kwantawa har sai sun ga bayansu.
Idan kuwa za su kai tunaninsu nesa za su gane akwai rai akwai mutuwa, idan su ne yau ba su ne gobe ba, kuma na san duk namiji mai hankali isashe ba zai so yaransa su tagayyara bayan mutuwarsa ba. Don haka neman na kai ga mata yake da matuƙar muhimmanci tun ma kana raye bare ka mutu.
Ta hanyar gina matanku ne kawai za ku iya samun tabbacin ‘ya’yanku ba za su tagayyara bayan mutuwarku. Don haka bai zama faɗuwa ba don ka gina matarka tare da ba ta damar neman na kai ba, koda kuwa kai ne za ka zaɓa mata irin sana’a ko aikin da ka ke so ta yi. Wannan wani hannun jari ne da kai karan kanka za ka iya cin moriyarsa bare kuma ‘ya’yanka wanda suka kasance ‘ya’yan cikinta.
A wata fuska kuwa laifin na mata ne, domin akwai matan da suka zaɓi zaman kashe wanda don lalaci, kuma ba wai ba su da hanya ko lafiyar nema ba. Wasu ma mazan za su ƙulla masu sana’a suna cinyewa har su gaji su sa masu ido. Wasu kuwa mazan ba su ba, amma sun ba su damar nema irin wanda suke so. Amma sai su zaɓi ƙin yi saboda ƙaramin tunanin da suke da shi. A tunaninsu ba sa buƙatar yin komai tunda ana yi masu, sun manta yau da gobe sai Allah, kuma akwai rai akwai mutuwa.
A wani ɓangare guda kuwa, mata na samun matsala ta rashin tsaro, kasancewar maigida wani maigadi ne ga iyalansa. Suna samun nutsuwa, su yi barci cikin kwanciyar hankali a sa’ilin da suke da masaniyar mijinsu na cikin gidan koda kuwa ba a ɗakin matar tasa ya kwana ba.
Kada in ja ku da nisa, shafin Gimbiya na jaridar Blueprint Manhaja ya nemi jin ta bakin ɗaya daga cikin matan da suka rasa mazajensu domin ciwo ne da ba wanda ya san yadda yake sai wanda ya taɓa ɗanɗanawa.
MANHAJA: Hajiya Sa’adatu Kankia, a matsayinki ta wadda ta rasa mijinta, ya za ki iya misalta rayuwar mace a lokacin da ta yi rashin maigidanta?
SA’ADATU KANKIA: Masha Allah, gaskiya na ji daɗin wanna ‘topic’ ɗin domin gaskiya akwai abubuwa sosai a cikin rayuwar matar da mijinta ya rasu, saboda akwai bambanci sosai tsakanin wadda aka saki da wadda mijin ya mutu.
Rayuwar mace bayan mutuwar mijinta, wata rayuwa ce da ke taɓa dukkan ɓangarori na rayuwarta, akan wannan dalilin nike tausayawa da yi matar da mijinta ya mutu ya barta kallon abar tausayi, musammam idan ya kasance ba ta aiki, kuma ba ta da ƙwaƙƙwarar sana’a.
Mutuwar miji, wani ciwo ne da sai matar da abin ya faru da ita ne take sanin yadda ciwon yake, saboda wani yanayi ne da ke taɓa rayuwar mace ta kowane ɓangare, ƙalubale iri daban-daban, matsalolin da ba ta taɓa tsammani ba za su taso mata, tun daga matsalar cikin gidanta, ta dangin miji, tarbiyyar yara, hidimar iyali, ga kuma babban ƙalubale na maza da za su taso da maganar sonta, amma kashi casa’in bisa ɗari ba so ba ne, sha’awa ce, za su zo kamar da gaske sonta suke yi, ana taimaka mata, sai ta saki jiki, sai su bijiro mata da wata buƙata, saboda suna ganin bazawarace, tasan aure, don haka ba zata iya haƙura ba yanzu da ba ta da miji. Abin takaici da yawansu makusantan mijin ne, abokanshi ko ‘yan uwanshi.
Wannan matsalar ta neman macen da mijinta ya rasu, tafi komi zama ƙalubale ga rayuwarta, sai kuma ta abinda za ta yi hidimar iyalinta, wanda akasari anfi yin amfani da wannan damar wajen kawo mata wata buƙata ta daban.
Da wahala ta samu mai taimaka mata domin Allah, don haka an saka shakku da tsoro a zukatan mata da yawa, wasu kuma an dulmiyar da su saboda ba su da madafa.
Sai kuma ƙalubale na tsangwama da tsana daga dangin miji, wanda akasari ni a fahimtata ana ƙirƙirar hakan ne don kada a rinƙa taimaka masu, sai abar mace tai ta wahala da yara.