
Daga BELLO A. BABAJI.
A ranar Asabar ne Mai bai wa shugaban ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ya miƙa sama da mutane 58 da aka ceto daga hannun ƴan bindiga ga Gwamnatin Jihar Kaduna bayan waɗansu atisayen haɗaka da jami’an tsaro suka gudanar.
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa shi ya jagoranci miƙa mutanen ga shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin, Sani Limankila wanda shi ya wakilci Gwamna Uba Sani na jihar.
Janar Musa ya ce babu wani kuɗin fansa da aka biya wajen ceto su waɗanda dakarun tsaro ne suka bi salo daban-daban wajen ayyukan ceto mutanen.
Ya nuna muhimmancin aiki kafaɗa-da-kafaɗa a kowanne mataki – daga Fadar shugaban ƙasa da ofishin NSA zuwa Ma’aikatar Tsaro da Gwamnatin Kaduna. Ya na mai cewa hakan ya taimaka wajen nasarar ceto mutanen.
Babban Hafsan Tsaron ya kuma jaddada cewa kowane ɗan Nijeriya na da rawar da zai taka wajen tabbatar da tsaro wanda matuƙar ba a samu aiki tare ba, to zai yi wahala a yi nasara.
Har’ilayau, ya kuma gargaɗi maɓarnata da ke yunƙurin haifar da koma-baya ga ƙoƙarin da gwamnati ke yi, ya na mai cewa jami’an tsaro na aiki tuƙuru wajen tabbatar tsaro ga rayuka da dukiyoyin duka ƴan Nijeriya.
