
Daga BELLO A. BABAJI
Manyan sanannun ƴan ƙasa da wasu ƴan Nijeriya sun haɗu a Jihar Kano don halartar ɗaurin auren ƴar jigon jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso.
An gudanar da bikin ɗaurin auren ne tsakanin Dakta A’isha Rabi’u Musa Kwankwaso da Injiniya Fahad Ɗahiru Mangal wanda ɗa ne ga shahararren Attajiri, Alhaji Ɗahiru Mangal na Jihar Katsina.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da; Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima; tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo; tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; da tsohon shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki.
Sauran sun haɗa da; tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Ahmed Maƙarfi; Sanata Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan Zamfara; Sanata Abdul Ahmed Ningi da kuma tsohon gwamnan Jihar Kebbi, Adamu Aliero.
Haka kuma, akwai Lucky Igbinedion, Mahmud Shinkafi, Isa Yuguda, Victor Atta da kuma Achike Udenwa.
