Daga RABIU SANUSI a Kano
Jam’iyyar NNPP ta Jihar Kano ta faɗa cikin rikici, inda har ta kai ga dakatar da Sakataren Gwamnatin Jihar Dakta Abdullahi Baffa Bichi, da Kwamishinan Sufuri na jihar Kano Muhammad Diggwal, daga cikin jam’iyyar.
Shugaban Jam’iyyar NNPP a Kano Dakta Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a cikin daren Litinin.
Hashim Dungurawa, ya ce dakatar da ƙusoshin gwamnatin jihar Kanon su biyu,ya biyo bayan zargin keta alfarmar jagoranci, da ta Jam’iyya, da kuma keta alfarmar gwamnati, a don haka ne suka ɗauki matakin ba tare da yin wasa ba akai.
“Jagorancin shugabancin jam’iyyarmu na ƙananan hukumomin da mutane biyun suka fito sun gabatar mana da ƙorafe-ƙorafe kan ƙusoshin gwamnatin biyu, akan zarge-zarge da ake musu ya sa muka ɗauki matakin dakatar da su, har sai mun gama bincike, inji Dungurawa.
Sulaiman ya ƙara da cewar dakatar da Abdullahi Baffa Bichi da Muhammad Diggwal ta fara aiki ne daga ranar Litinin 14 ga watan Oktoban 2024, kamar yadda jam’iyyar ta samu ingantattun shawarwari akan zargin da ake musu.
A wani jawabin kuma sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya barranta kansa da wata kungiyar magoya baya dake ikirarin yana da hannu wajen batutuwa dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani da ake cema ”Abba tsaya da ƙafafunka’.
Baffa Bichi ya ce babu wata ƙungiya da yake da hannu ciki makamanciyar hakan dan haka ba shi da wata alaƙa da ita.
Sakataren gwamnatin ya ce idan banda ƙungiyar (One to Tell Ten) da yake da ya yi kamfen ɗin Shugaban ƙasa a faɗin jihohin Arewa 19 da ake da su.
”Muna yi wa gwamna biyayya matuƙa da jagoranmu na ɗarikar Kwankwasiyya na duniya Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso bisa haka ni bani da wata masaniyya kan wancan batun wata ƙungiya da ake alaƙantata da ni.
A nasa jawabin ɗan takarar kujerar Jam’iyyar NNPP na ƙaramar Hukumar ta Bichi Hon. Hamza Sule mai Fata ya ce a tsakaninsu da Baffa Bichi babu wata matsala.
Hon. Hamza Mai Fata ya bayyana haka ne yayin kammala wani zaman rufe kofa da ya gudana da gwamna Abba Kabir da Sakataren Gwamnatin da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano har ma da sauran masu ruwa da tsaki.
”Mu masu biyayya ne ga jam’iyyarmu ta NNPP da tafiyar Kwankwasiyya, don haka daga yau ba zan ƙara riƙe wannan a matsayin wani abu daban ba.
”Gaskiya mun godewa mai girma gwamnanmu bisa jajircewarsa wajen haɗa kan magoya bayanmu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa wannan wuta dai na da alaƙa da hana ɗan takarar shugaban ƙaramar hukuma da ya fito daga tsagin shi ya sa wutar wannan lamari takara ruruwa.
Sai dai ba tun yau ba ana ganin irin hakan za ta ƙara ruruwa idan har ba a ɗauki matakin gaggawa ba to lallai wankin hula zai kawo tsalen badake a wannan jam’iyyar NNPP.
Haka kuma a wata majiyar an ce jam’iyyar ta NNPP ta dakatar na kwamiahinan Sufuri na jihar Kano Hon Muhammad Digol bisa dalilin rashin kame baki daga sakin magana da rashin nuna biyayya ga uwar jam’iyya ta jihar Kano.
Ya zuwa yanzu dai dukkan kallo ya koma sama sakamakon dakatar da manyan fulogan da ake kallon karansu ya kai tsaiko a wannan jam’iyya da shugabancinta ya samu damar dakatar da su a tafiya, yayin da babbar jam’iyyar adawa wato APC take zawarcin da yawansu.
ɗan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP kuma jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba zai yi magana kan rikicin cikin gida da ke faruwa a jam’iyyar a Jihar Kano.
Da ’yan jarida suka tambaye shi game da rikicin a gidansa da ke Miller road a Kano, a ranar Talata, Kwankwaso ya ce ba shi da abin cewa.
“Ba na son yin magana game da batun. Don Allah kada ku sanya ni cikin abin da ba na da alaƙa da shi. Shugaban jam’iyya ya riga ya yi magana, kuma yana ci gaba da magana a kai, ku tuntuɓe shi,” in ji shi.
Manhaja ta ruwaito yadda rikicin cikin gida ya sanya shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Abdullahi Baffa Bichi da Kwamishinan Sufuri, Muhammad Diggol.
Shugaban jam’iyyar, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya bayyana cewa an dakatar da su ne saboda zargin rashin girmamawa jam’iyyar.
Kazalika, ya ce sun yi amfani da muƙamansu ba bisa ƙa’ida ba, da rashin biyayya ga jam’iyyar.
Dakatarwar ta biyo bayan wani yunƙurin da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi na sasanta sakataren gwamnatin da ‘yan mazaɓarsa da suka samu matsala.
Haka kuma, sakataren ya nesanta kansa daga wata ƙungiya da ke neman raba Gwamna Yusuf da Kwankwaso, wanda ta ke yi wa gwamnan taken “Abba, ka tsaya da ƙafarka.”
