Daga ZUBAIRU JIBIA a Abuja
Zaɓen fidda gwani na kai tsaye (Direct Primaries) na Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) domin tantance ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazaɓar Igabi a jihar Kaduna ya fuskanci ce-ce-ku-ce, zarge-zargen rashin adalci da kuma rikicin cikin gida, lamarin da ya jefa mambobin jam’iyyar cikin ruɗani.
Zaɓen wanda ya haɗa da fafatawa tsakanin ESɓ Hon. Dr. Sani Abdulkadir Dakaci da Hon. Hussain Muhammad Jalo, ya gamu da matsaloli masu yawa da kuma rashin ingantaccen tsari a wurare daban-daban da aka tsara gudanar da zaɓen a ƙaramar Hukumar Igabi.
Binciken da aka gudanar daga wasu rumfunan zaɓe ya nuna cewa ba a gudanar da zaɓen yadda ya kamata ba bisa ƙa’idojin jam’iyyar APC da kuma tsarin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta tanada.
Rahotanni daga wuraren zaɓen sun tabbatar da cewa jami’an jam’iyyar da wakilan da aka tura domin kula da zaɓen ba su bayyana a mafi yawan rumfunan zaɓe ba. Haka kuma, wakilan INEC da ake sa ran za su sa ido kan yadda ake gudanar da zaɓen ba a gan su ba yayin da ake ikirarin gudanar da zaɓen.
Sai dai duk da matsalolin da suka dabaibaye tsarin zaɓen, rahotannin siyasa daga cikin al’umma da masu ruwa da tsaki sun nuna cewa Hon. Sani Abdulkadir Dakaci na da babban goyon baya da farin jini a tsakanin mambobin APC da al’ummar ƙaramar Hukumar Igabi.
Masu sharhi kan harkokin siyasa a yankin sun bayyana cewa idan aka gudanar da sahihin zaɓe cikin gaskiya da adalci, akwai yiwuwar Dakaci ya samu gagarumar nasara.
A gefe guda kuma, rikicin ya ƙara tsananta bayan da wasu magoya bayan Hon. Hussain Muhammad Jalo suka yi iƙirarin cewa wasu manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun bayar da umarni ga shugabannin APC da su amince da Jalo a matsayin ɗan takarar sulhu (Consensus Candidate) na jam’iyyar.
Wannan iƙirari ya haddasa rashin jituwa tsakanin magoya bayan ‘yan takarar biyu tare da janyo muhawara mai zafi a tsakanin mambobin jam’iyyar a yankin.
Da yake mayar da martani, ESɓ Hon. Dr. Sani Abdulkadir Dakaci ya yi fatali da batun yarjejeniyar sulhu tare da jaddada cewa babu wani sahihin zaɓe da aka gudanar da zai ba wa kowa damar bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara.
Dakaci ya bayyana cewa duk wani yunƙuri na bayyana ɗan takara ba tare da bin ƙa’ida da tsarin dimokuraɗiyya ba, ya saɓa wa manufofi da ƙa’idojin jam’iyyar APC.
Ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyar da su tabbatar da adalci da gaskiya domin kare mutuncin APC da kuma hana rikicin cikin gida da zai iya shafar haɗin kan jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027.
Lamarin dai na ci gaba da jan hankalin mambobin APC da masu bibiyar siyasa a jihar Kaduna, inda da dama ke kira ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa da ya shiga tsakani domin warware rikicin tare da tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin zaɓen fidda gwani.
