Rikicin Masarautar Kano: Ba a yi wa Bayero adalci ba, cewar Kotun Ɗaukaka Ƙara

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin cewa, Babbar Kotun Jihar Kano ba ta yi wa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, adalci ba a shari’ar da ya ke gudanarwa tsakaninsa da Gwamnatin Jihar Kano kan tuɓe shi da gwamnatin ta yi ba.

A yayin da ya ke yanke hukuncin ranar Alhamis, Alƙali Mohammed Mustapha, wanda ya jagoranci sauran alƙalan kotun uku, ya bai wa Alƙalin Alƙalan Jihar Kano umarnin ya naɗa sabon alƙali, don sake gudanar da shari’ar, wacce tun farko ta wakana a ƙarƙashin Alƙali Amina Adamu Aliyu saboda rashin bai wa ɓangaren Aminu Bayero cikakken ‘yancin kare kai.

Idan za a iya tunawa, lauyoyin Bayero sun fice daga cikin kotu gabanin Alƙali Amina Aliyu ta yanke hukunci a shekarar bara bisa zargin ba za a yi musu adalci ba.

A lokacin, Mai Shari’a Amina ta hukunta cewa, Bayero ya daina ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, saboda sabuwar dokar da Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta ƙirƙira, wacce ta rushe masarautu biyar da aka ƙirƙira a jjhar kuma Gwamnan Jihar Kano ya rattaɓa wa hannu, sannan ya sauke Aminu Ado Bayero, ya naɗa Muhammadu Sanusi II, jim kaɗan da sanya hannun.

Mai Shari’a Mustapha ya ce, ci gaba da sauraron shari’ar tare da yanke hukuncin da alƙalin ta yi ya saɓa wa ƙa’idar shari’a ta yin adalcin sauraron kowane ɓangare. Don haka sai an sake shari’ar ɗungurungum ɗinta kuma a ƙarƙashin wani alƙalin daban.

Sai dai a wani ɓangaren hukuncin kuma, Alƙali Mustapha ya yanke hukuncin cewa, Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ƙarƙashin Alƙali Liman ta yi azarɓaɓi wajen sauraron shari’ar da Aminu Babba Ɗan Agundi ya kai yana mai ƙalubalantar zargin tauye haƙƙinsa da aka yi wajen sauke Bayero da shi kansa.

Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙarar sun ce, Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron komai kan abin da ya shafi masarautu a Nijeriya. Don haka sun rushe hukunci da ta yanke na dawo wa Bayero mulkin Masarautar Kano.

By ukarofi