Rikicin PDP: ‘Yan sanda sun rufe hanyar shiga wurin taron ƙaddamar da takarar Jonathan

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP ya sake ɗaukar wani sabon salo bayan da jami’an ‘yan sanda suka tare hanyar shiga dandalin taron da ɓangaren jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ya shirya a Abuja domin amincewa da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Rikicin PDP ya samo asali ne tun bayan shan kayen da jam’iyyar ta yi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda saɓani kan shugabanci da ikon tafiyar da harkokin jam’iyyar ya haifar da ɓangarori masu adawa da juna. Wani ɓangare na samun goyon bayan Tanimu Turaki da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar, yayin da ɗayan ɓangaren ke da alaƙa da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike.

Ɓangaren Turaki ya daɗe yana yaƙin neman amincewa da Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a 2027, yana mai jaddada cewa har yanzu mamba ne na jam’iyyar kuma yana da damar neman tikitin takara. Sai dai Jonathan bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba, duk da kiraye-kirayen da ƙungiyoyi daban-daban ke yi masa na komawa fagen siyasa.

Tashin hankalin ya ƙara ƙamari ne bayan da ‘yan sanda suka mamaye hanyar zuwa A-Class Event Centre, wurin da aka shirya gudanar da taron. Yayin da ɓangaren Turaki ke zargin wasu masu faɗa a ji da ƙoƙarin hana taron gudana, ɓangaren da ke goyon bayan Wike ya dage cewa taron ba shi da sahalewar sahihan hukumomin PDP. Lamarin na ƙara nuna irin ƙalubalen da jam’iyyar ke fuskanta wajen hada kan mambobinta gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

By ukarofi

Leave a Reply