Gumi ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan masu zargin sa da goyon bayan ’yan bindiga

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi, ya yi kakkausar suka tare da musanta zarge-zargen da ke danganta shi da kalaman da ake ganin suna goyon baya ko kare ayyukan ’yan bindiga a Nijeriya.

Malamin mai hedikwata a jihar Kaduna ya bayyana irin waɗannan zarge-zarge a matsayin ƙarya, karkatar da bayanai da kuma muguwar manufa da aka shirya domin ɓata masa suna.

Sheikh Gumi, wanda sau da dama ya kasance cikin tattaunawar ƙasa kan matsalar tsaro da kuma tattaunawa da masu ɗauke da makamai a Arewacin Nijeriya, ya ce wasu mutane da kafafen sada zumunta sun karkatar da kalamansa da gangan domin haddasa rarrabuwar kai, son zuciya da neman jawo hankalin jama’a.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa tare da wallafa ta a shafinsa na sada zumunta da aka tabbatar da sahihancinsa a ranar Asabar, malamin ya nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da fassara ra’ayoyinsa ba daidai ba a hirarrakin kafafen yaɗa labarai, wa’azozi da kuma muhawarar da ake yi kan matsalar tsaro a ƙasar nan.

A cewarsa, wasu ƙungiyoyi masu son zuciya, mutane masu nuna wariya da masu ƙirƙirar bayanai a intanet suna ci gaba da yaɗa bayanai masu ruɗani da kanun labarai masu tunzura jama’a domin samun karɓuwa da yawan masu ziyartar shafukansu, ba tare da la’akari da halin da waɗanda rikicin tsaro ya shafa suke ciki ba.

Malamin ya bayyana sarai cewa bai taɓa goyon baya, karewa ko inganta ayyukan ’yan bindiga a Nijeriya ko wani wuri ba, yana mai cewa duk wani abu da ke nuna hakan ba daga gare shi ya fito ba.

Ya ce, bidiyoyi, gajerun faifan bidiyo da aka gyara, saƙonnin sada zumunta da rubuce-rubuce da ake yaɗawa da sunansa an yi musu kwaskwarima ne ko kuma an cire su daga ainihin ma’anarsu domin ƙirƙirar mummunar fahimta a kansa.

“Na bayyana a sarari cewa duk wani faifan bidiyo, rubutaccen bayani ko saƙo da ake dangantawa da ni kai tsaye ko a fakaice, wanda ke nuna cewa ina goyon baya ko kare ayyukan ’yan bindiga, ba daga gare ni ya fito ba,” in ji sanarwar.

Sheikh Gumi ya jaddada cewa duk tsoma bakinsa da ya yi a batun tsaro tsawon shekaru yana da nufin samar da mafita mai ɗorewa da lumana, ba ƙarfafa ayyukan ta’addanci ba.

Da alama malamin ya nuna fushinsa kan yadda ake ci gaba da yaɗa abin da ya kira ƙage da ƙarya a kansa, inda ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana yaɗa batanci a kansa zai iya fuskantar matakin shari’a.

Ya kuma buƙaci jama’a, kafafen yaɗa labarai da hukumomin gwamnati da su yi watsi da bayanan bogi da aka danganta da sunansa.

Malamin ya ƙara da cewa karkatar da tattaunawa kan batutuwan tsaro domin manufofin siyasa ko na ƙabilanci na ƙara haddasa rarrabuwar kai tare da hana ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a yankunan da rikici ya shafa.

Ya ce, tattaunawa mai ma’ana, rahotanni na gaskiya da kuma jawabi cikin hikima suna da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin tsaro masu sarƙaƙiya da Nijeriya ke fuskanta.

Sheikh Gumi ya kuma sake bayyana biyayyarsa da ƙaunarsa ga Nijeriya, yana mai cewa ƙasar tana da ɗimbin baiwa da albarkatu duk da ƙalubalen da take fuskanta a halin yanzu.

“Ni ɗan ƙasa ne mai biyayya ga ƙasata Nijeriya, ƙasar da na yi imani tana da baiwar da babu kamarta a duniya,” in ji shi.

A tsawon shekaru, malamin ya kasance ɗaya daga cikin fitattun muryoyi masu jawo cece-kuce a tattaunawar da ta shafi ’yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Yamma, musamman saboda ganawarsa da wasu masu ɗauke da makamai domin ƙarfafa tattaunawa da rage tashin hankali.

Masu sukar sa sun sha zarginsa da nuna tausayi ga ’yan bindiga, yayin da masu goyon bayansa ke cewa matakansa wani ɓangare ne na yunƙurin samar da zaman lafiya da kuɓutar da mutanen da aka sace.

A ƙarshe, Sheikh Gumi ya nuna alhini ga al’ummomin da rikice-rikice, kashe-kashe da garkuwa da mutane suka daidaita a faɗin ƙasar nan, inda ya yi kira da a haɗa kai a matakin ƙasa da na ƙasa da ƙasa domin kawo ƙarshen rashin tsaro da dawo da zaman lafiya.

Ya ce tushen matsalar tsaro a Nijeriya ya samo asali ne daga jahilci, talauci, wariya da rashin adalci a cikin al’umma.

A cewarsa, samar da zaman lafiya mai ɗorewa zai buƙaci gaskiya, adalci da cikakken jajircewa daga shugabanni da al’umma baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply