Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Fadar Shugaban ƙasa ta kare yadda bashin Nijeriya ke ƙaruwa a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai cewa har yanzu ƙasar na da ƙarfin ci gaba da karɓar rance duk da damuwar da jama’a ke nunawa kan bashin cikin gida da na ƙasashen waje.
Mai magana da yawun Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a dandalin ɗ yayin da yake mayar da martani kan masu sukar yadda bashin Nijeriya ke ƙaruwa a gwamnatin Tinubu.
A cewarsa, mutane da dama da ke nuna damuwa kan bashin ƙasar ba su da cikakkiyar fahimta kan tattalin arziki da tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati.
“Nijeriya ba ta ci bashin da ya wuce ƙima ba idan aka kwatanta da ƙasashe kamar Masar, Afirka ta Kudu da kuma Senegal,” inji Onanuga.
Ya ƙara da cewa, Nijeriya har yanzu ƙasa ce da ake iya amincewa da ita wajen karɓar rance, tana da damar ci gaba da samun bashi domin gina muhimman ababen more rayuwa.
“Yawan surutan da ake yi kan bashin ƙasa ba tare da dalili ba alama ce ta rashin fahimtar tattalin arziki da harkokin kuɗi,” ya bayyana.
Onanuga na mayar da martani ne ga wani mai amfani da shafin ɗ mai suna Akinwumi, wanda ya kwatanta yawan bashin Nijeriya da na Masar da Afirka ta Kudu ta fuskar kaso da ake auna bashi da girman tattalin arziki, wato debt-to-GDP ratio.
A cewar bayanan da aka wallafa, ana hasashen bashin Masar ya haura dala biliyan 400 yayin da tattalin arzikinta yake kusan dala biliyan 390, lamarin da ya nuna bashinta ya zarce kaso 100 cikin 100 idan aka kwatanta da GDP ɗinta.
Haka kuma, bashin Afirka ta Kudu ya kai kusan dala biliyan 580 yayin da GDP ɗinta yake kusan dala biliyan 420, wanda hakan ke nuna kaso 135 cikin 100.
Sai dai a Nijeriya, an kiyasta jimillar bashin gwamnati zuwa kusan dala biliyan 110 tare da GDP mai kusan dala biliyan 340, wanda hakan ke nuna kaso 35 cikin 100 kacal.
“Duk da haka wasu na ci gaba da kiran Nijeriya babbar ƙasar da ta fi karɓar bashi a duniya,” in ji bayanin.
Wannan martani na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ci gaba da nuna damuwa kan yadda gwamnatin Tinubu ke ci gaba da karɓar bashi duk da tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki da ake fama da shi a ƙasar.
Tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, gwamnatin Tinubu ta samu da kuma neman sababbin rance daga cikin gida da ƙasashen waje domin tallafa wa ayyukan gine-ginen more rayuwa, farfaɗo da tattalin arziki da kuma cike giɓin kasafin kuɗi.
A baya-bayan nan, gwamnatin tarayya ta nemi sababbin rance na biliyoyin daloli daga cibiyoyin kuɗi na duniya ciki har da Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka, tare da ƙara yawan bashin cikin gida ta hanyar takardun bashi da sauran hanyoyin tara kuɗaɗe.
Gwamnatin ta dage cewa bashin ya zama dole domin samar da kuɗaɗen ayyukan lantarki, sufuri, noma da shirye-shiryen tallafawa jama’a.
Sai dai masu sukar gwamnati na ci gaba da gargaɗin cewa yawan kuɗin biyan bashi, hauhawar farashi da kuma raunin darajar naira na ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin matsin lamba.
