Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya sake kafa wani sabon tarihi a duniya bayan jagorantar ƙungiyarsa ta Al-Nassr zuwa gagarumar nasarar 4-2 a kan Al-Shabab.
Ronaldo ya cimma wannan bajinta ne bayan ya zura wa dukkan ƙungiyoyin da ya kara da su a gasar Saudi Pro League ta bana ƙwallo, abin da ya ƙara tabbatar da matsayinsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ’yan wasa mafiya tarihi a duniyar tamaula.
Kafin wasan, Al-Shabab ita ce kaɗai ƙungiyar da Ronaldo bai samu damar zura wa ƙwallo ba a kakar 2025/2026. Sai dai tauraron ɗan wasan ya kawo ƙarshen hakan bayan da ya jefa ƙwallo a minti na 75 da fara wasan, wanda hakan ya sa ya kammala zura wa dukkan abokan hamayyarsa a gasar ƙwallaye.
Wasan ya kuma zama wata dama da Ronaldo ya ƙara kafa wasu manyan tarihi a harkar ƙwallon ƙafa.
Tauraron ɗan wasan ya zama mutum na farko a tarihin ƙwallon ƙafa da ya ci ƙwallaye 100 ko fiye da haka a ƙungiyoyi huɗu daban-daban da ya taka wa leda.
ƙwallon da ya ci wa Al-Shabab ita ce ta 100 da ya ci wa Al-Nassr a gasar Saudi Pro League, lamarin da ya haɗa shi cikin jerin ’yan wasan da suka kafa manyan tarihi bayan ya taba cin ƙwallaye 101 a Manchester United da kuma 311 a Real Madrid.
Haka kuma Ronaldo ya zama ɗan wasa na farko daga wata ƙasa daban da ya kai ƙwallaye 100 a gasar firimiya ta Saudiyya.
Da wannan sabon ƙwallon, adadin ƙwallayen da Ronaldo ya ci a dukkanin wasannin da ya buga a rayuwarsa sun kai 971 a hukumance.
Nasarar da Al-Nassr ta samu ta sa ƙungiyar ta ci gaba da zama a saman teburin gasar da tazarar maki biyar tsakaninta da abokan hamayya, lamarin da ya sa masu sharhi ke ganin Ronaldo ba wai kawai yana neman lashe kofin gasar Saudiyya na farko ba ne, har ma yana daf da kafa tarihin kaiwa ƙwallaye 1,000 a rayuwarsa ta tamaula.
Ana sa ran wasan da Al-Nassr za ta fafata da babbar abokiyar hamayyarta Al-Hilal a mako mai zuwa zai zama mai matuƙar muhimmanci wajen tantance wanda zai lashe gasar bana.
