2027: Matasan Arewacin Nasarawa sun bayyana goyon bayansu ga Dakta Silas Agara

Spread the love

Daga JOHN D WADA a Keffi

Shugabannin matasa a yankin mazaɓun sanatan Arewacin jihar Nasarawa sun bayyana goyon bayansu na musamman ga ɗan takarar kujerar sanata a ‘yankin wato Dr. Silas Ali Agara a zaɓen kujerar sanatan don saka masa da alherin tallafawa matasa da cigaban al’umma da suka ce ya daɗe yana yi.

Shugabannin sun bayyana haka ne ranar Juma’a 15 ga Mayu 2026 bayan wani taron masu ruwa da tsaki na shugabannin matasan ƙabilu daban-daban da wakilan matasa daga ƙauyuka da ƙananan hukumomi a faɗin yankin wanda aka gudanar a otel din Esslah Guest House a Akwanga.

A cikin sanarwar da aka fitar a ƙarshen taron shugabannin matasan sun ce yankin a yanzu haka na buƙatar wakilci mai hangen nesa da sauƙin kusanci da kuma mai kula da buƙatun jama’a a majalisar dattawa don cimma burin cigabanta.

Ƙungiyar tace goyon bayansu ga Dr. Agara ya dogara ne akan ƙudirorin sa na tallafa wa matasa da cigabansu ta hanyar tarihin hidima da ƙwarewar shugabanci da hankali ga cigaban al’umma a matakai daban daban da fahimtar buƙatun gida da hangen nesa na mulki mai tafiya da kowa da mayar da hankali kan cigaban ilimi da damar tattalin arziki da cigaban al’umma mai ɗorewa da sauransu.

Shugabannin matasan sun kuma yi amfani da damar inda suka yi alkawarin wayar da kan matasa a dukka ƙananan hukumomi ‘yankin na Arewacin jihar ta Nasarawa domin su shiga tsarin zaɓe da himma tare da mara wa shugabanci na gaskiya ƙarƙashin jagorancin Dr. Silas Ali Garage a lokacin zaɓen.

Haka kuma sun kira ga matasa ‘yan siyasa da sarakuna da malamai da ƙungiyoyin mata dana farar hula da su zauna da junansu lafiya da haɗa kai da nuna ɗabi’un dimokuraɗiyya kafin lokacin da kuma bayan zaɓen.

Sun cigaba da bayyana cewa “Wannan sanarwa tana wakiltar murya guda ne tare da burin haɗin gwiwa na matasan sanatan Arewacin Nasarawa domin samun wakilci nagari mai tabbatar da cigaba da mulki mai riƙon amana da makoma mai albarka ga kowa,” in ji sanarwar.

By ukarofi