Masalahar fidda ɗan takarar Gwamnan Gombe zalunci ne — Pantami

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Aliyu Isa Pantami, ya bayyana cewa tsarin da aka bi wajen tsaida ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar APC ta hanyar maslaha bai bi ka’idojin doka da adalci ba.

Pantami, wanda ke neman takarar gwamnan jihar Gombe, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai bayan ayyana Alhaji Jamilu Isyaku Gwamna a matsayin ɗan takarar APC na zaɓen 2027.

Ya ce tsarin maslaha ko “consensus” yana da ka’idoji guda uku da dole sai an bi kafin a ce an yi sahihin tsaida ɗan takara.

A cewarsa, ka’idojin sun haɗa da: Amincewar dukkan masu ruwa da tsaki, Tattaunawa ko wakilcin duk masu neman takara, da kuma bin tanade-tanaden dokar zaɓe.

Pantami ya ce babu ɗaya daga cikin waɗannan ka’idoji da aka bi a tsarin da aka yi a Gombe.

“Abin da aka yi zalunci ne kuma son rai ne. Ni ba zan amince da zalunci ba, ko da kuwa hakan zai kai ga rasa raina,” inji Pantami.

Ya yi nuni da cewa dokar zaɓe ta shekarar 2026 ta tanadi hanyoyin gudanar da maslaha a sashe na 81, 84 da 87, amma ba a mutunta waɗannan tanade-tanade ba.

Sai dai duk da ƙorafin Pantami, jam’iyyar APC ta ayyana Alhaji Jamilu Isyaku Gwamna a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar Gombe domin tunkarar zaɓen 2027.

By ukarofi