Inganta harkar ilimi na daga cikin manufofin Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Jahun — Abdullahi Abubakar

Spread the love

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA a Kano

Shugaban Kwalejin Nazarin Harkokin Lafiya, Kimiyya da Fasaha ta Jahun da ke Jihar Jigawa, Malam Abdullahi Abubakar, ya bayyana cewa inganta harkar koyo da koyarwa na daga cikin manyan manufofin kwalejin domin samar da ƙwararrun jami’an lafiya da za su taimaka wajen bunƙasa harkar kiwon lafiya a ƙasa.

Malam Abdullahi Abubakar ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa, inda ya ce bayar da cikakken goyon baya ga ilimin yara mata musamman a fannin lafiya na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ingantattun ma’aikatan lafiya da za su kula da lafiyar mata da yara, tare da samar da ayyukan yi ga matasa bayan kammala karatunsu.

Ya ce a ƙarƙashin gwamnatin Jihar Jigawa ta Gwamna Malam Umar Namadi, kwalejin ta samu gagarumar nasara ta fuskar bunƙasa ilimi da inganta tsarin gudanarwa.

A cewarsa, daga cikin nasarorin da kwalejin ta samu akwai sahalewar shirye-shiryen bayar da takardun digiri guda 12 daga Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta ƙasa (NBTE), tare da ƙarin girma ga ma’aikata da kuma inganta tsarin koyarwa da gudanar da harkokin ilimi.

Ya ƙara da cewa kwalejin na gudanar da shirye-shirye guda 12 da NBTE ta amince da su, inda ya bayyana cewa wasu ƙalubale kaɗan da aka fuskanta yayin tantance wasu daga cikin shirye-shiryen tuni an shawo kansu cikin nasara.

Malam Abdullahi Abubakar ya yaba wa gwamnatin Jihar Jigawa bisa ƙoƙarin da take yi wajen tallafa wa fannin ilimi, musamman ta hanyar samar da ingantattun shirye-shirye da kayan aiki domin sauƙaƙa wa ɗalibai harkokin karatu.

Ya ce wannan ci gaba ya bai wa ɗalibai, musamman yara mata ‘yan asalin jihar, damar samun ingantaccen ilimi da horo a fannin lafiya cikin yanayi mai kyau.

Haka kuma, ya bayyana cewa kwalejin ta samar da tsarin gudanar da karatu ta yanar gizo, wanda ya haɗa da yin rajista da sauran harkokin karatu cikin sauƙi da kwanciyar hankali, domin tabbatar da ingantaccen tsarin ilimi da ya dace da zamani.

By ukarofi