’Yan siyasa su kula da sha’anin marayu da masu buƙata ta musamman – Sani Kuɗai

Spread the love

Daga ABDULLAHI SANI DOGUWA

An buƙaci attajirai da ’yan siyasa masu jagorantar al’umma a matakai daban-daban da su ƙara mayar da hankali wajen tallafa wa marayu, marasa galihu da masu buƙata ta musamman domin rage musu raɗaɗin rayuwa da kuma inganta walwalarsu.

Shugaban Gidauniyar Kowa Ya Ga Girman Na Gaba APC Youth Forum reshen Jihar Jigawa, Alhaji Sani Abdullahi Kuɗai, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya haɗa masu ruwa da tsaki da ’yan siyasa daga ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.

A cikin jawabin nasa, Alhaji Sani Abdullahi Kuɗai ya jaddada muhimmancin amfani da ribar dimokuraɗiyya wajen tallafawa masu ƙaramin ƙarfi a cikin al’umma, yana mai cewa hakan na ƙara haɗin kai da inganta rayuwar jama’a.

Ya bayyana cewa tun shekaru da dama gidauniyarsa ke gudanar da shirye-shiryen tallafawa matasa da mata da marayu da masu buƙata ta musamman ta hanyoyi daban-daban domin rage musu wahalhalun rayuwa.

A cewarsa, daga cikin tallafin da suke bayarwa akwai taimakawa matasa da jari domin dogaro da kai, bai wa mata jari na ƙananan sana’o’i, tallafawa zawarawa, da kuma kula da marayu da masu larura ta musamman.

Alhaji Sani Abdullahi Kuɗai ya ce abin da ya ƙara masa ƙwarin gwiwar gudanar da irin waɗannan ayyuka shi ne irin misalin tausayi da jin ƙai da yake gani daga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da kuma fitaccen ɗan kasuwa Alhaji Muhammadu Isah Gerawa, waɗanda ya bayyana a matsayin masu taimakon marasa galihu.

Ya ƙara da cewa taron ya kasance wata dama ta wayar da kan attajirai da ’yan siyasa game da muhimmancin tallafa wa mabukata domin samun ingantacciyar al’umma mai cike da tausayi da taimakon juna.

A yayin taron, an raba tallafi ga mutane 240 da suka haɗa da kekunan guragu ga masu buƙata ta musamman, kayan abinci ga zawarawa, da tufafi ga marayu da sauran marasa galihu.

Alhaji Sani Abdullahi Kuɗai ya bayyana cewa manufar tallafin ita ce rage wa mabukata ƙuncin rayuwa tare da ba su damar jin cewa suna cikin al’umma mai kulawa da juna.

Ya kuma sha alwashin ci gaba da faɗaɗa ayyukan gidauniyarsa domin taimakawa marasa galihu, yana mai cewa zai ci gaba da koyi da irin kyawawan ayyukan jin ƙai da manyan jagororin jihar ke yi.

Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai wakilin Gwamnan Jihar Jigawa, Hon. Salisu Seeker, da wakilin attajirin ɗan kasuwa Alhaji Muhammadu Gerawa, Isiyaku Isah Muhammadu, waɗanda suka yaba wa Alhaji Sani Abdullahi Kuɗai kan irin wannan ƙoƙari na taimakon al’umma.

Haka kuma, ɗan majalisar dokokin Jihar Jigawa mai wakiltar Birnin Kudu, Hon. Ishaƙ Soja, ya yaba da shirin tare da bayar da gudunmawar kuɗi har naira dubu dari biyu domin tallafawa marasa galihu.

Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin sun bayyana matuƙar farin cikinsu tare da yi wa Alhaji Sani Abdullahi Kuɗai addu’ar Allah ya ƙara masa lafiya da arziki domin ci gaba da taimakon al’umma.

By ukarofi