Rugujewar gine-gine a Nijeriya: Matsalar injiniyoyi ne ba ma su zane ba – Bashir Hanga

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban Ƙungiyar Masana Taswirar Vine-gine ta Ƙasa reshen jihar Kano, Arc. Bashir Hassan Hanga, ya bayyana cewa matsalar rushewar gine-gine da zaftarewar gadoji a Nijeriya ba laifin masana zana taswira ba ne, sai dai matsalar injiniyoyi musamman baragurbi, ‘yan kankanba masu sa kansu ba su ƙware a aiki ba saboda son zuciya a wannan aiki, wanda idan aka yi yakan ruguje ko kuma son zuciya da ha’inci da amaja.

Har’ila yau, ya ce hakan na faruwa ne kan sakaci da ganganci domin wani lokacin ya kan zama an rage kayan aiki, inda ake buƙatar siminti biyu a sa ɗaya, ko kuma rodi ana buƙatar kamar goma sai a yi amfani da guda takwas kuma gurin da za a ɗaura bene hawa sha biyar sai asa hawa 21 kamar yadda ta faru benen Legas a cewarsa, inda ya ruguje ya hallaka jama’a harda injiniyan aka rasa rayuka da dukiya.

Ya bayyana cewa babu hannun masana taswira a cikin wannan matsala, “mu za mu fitar da abu ne bisa ƙai’ida,” inji shi.

Haka kuma a ƙarshe ya ce wani abun sha’awa shi ne yadda matasa ɗalibai ke sha’awar wannan karatu na ilimin taswira tun daga ganin gini a unguwa ko cikin birane wanda dama aikin mu shi ne zana taswira duk wani abu da ake cewa muhalli kamar gina gari, unguwa, kamfanoni da kuma gidajen zama da ma’aikatu kuma shi ne babban bambancin mu da masu ilimin zane-zane su kowacce halitta sa iya zanawa kamar mutun, ko bishiya ko tsintsaye, dabbobi da makamantansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *