Rundunar soja ta cafke sojan da ya kashe wani ɗan zanga-zanga a Kaduna

Spread the love

Sojojin Najeriya sun kama sojan da ya kashe wani matashi mai shekara 16, mai suna Isma’il Mohammed, yayin da yake kokarin dakatar da wasu matasa ƙokarin fasa shagunan mutane a unguwar Samaru da ke Zaria da sunan zanga-zanga.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulɗa da jama’a na sojojin, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayar a ranar Laraba a Abuja.

Nwachukwu ya ce sojojin sun samu kiran gaggawa cewa wasu matasa sun taru a yankin Samaru na Zaria masu yawan gaske, suna ƙona tayoyi a kan titi suna jefa duwatsu ga jami’an tsaro.

“Da isar su wurin, matasan suka yi ƙoƙari wajen kai wa sojojin hari, wanda hakan ya sa wani soja ya harba bindiga domin tsoratar da matasan, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar wani matashi mai shekara 16, mai suna Isma’il Mohammed.

“An kama sojan da ya aikata wannan gangancin, kuma ana ci gaba da bincike a kansa a lokacin da ake rubuta wannan rahoton,” in ji shi.

A cewarsa, an binne wanda ya rasu bisa tsarin addinin Musulunci, tare da halartar manyan jami’an sojin Najeriya wajen janaizar.

By ukarofi