Rundunar sojojin sama a Katsina sun ceto mutane 62 daga hannun ‘yan bindiga a Ɗanmusa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A wata sanarwar da kwamishinan cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya fitar ya bayyana cewa yanzu haka mutane 16 cikin waɗanda aka ceto na amsar kulawa a asibitin Matazu.

Ya bayyana cewa sojojin sun sami nasarar kuɓutar da waɗannan mutane bayan sun kai hare haren ga wani sansanin ƴan bindigan da Muhammadu Fulani ke shugabanta a dajin Jigawa Sawai da yayi iyaka da Jihar Zamfara.

“Lugudan wuta da sojojin su kai ta kai wa sansanin ƴan bindigan ya sa jagoran ƴan ta’addan Muhammadu Fulani da mutanen sa suka ranta a na kare,haka ya ba sojojin dama suka kuɓutar da wannan mutane,”inji Dr Ɗanmusa.

Dr Nasiru Ɗanmusa ya bayyana cewa sojojin sun kai ɗauki ne a ƙananan hukumomin Bakori da Matazu bayan da gwamnatin jihar ta samu rahoton hare haren na ƴan bindiga a waɗannan wurare da yace a yanzu an fara samun zaman lafiya.

Ya ce nan bada jimawa ba gwamnati za ta miƙa waɗanda mutane da aka kuɓutar ga iyalan su.

Kwamishinan ya jinjina wa jami’an tsaro kan ƙoƙarin da suke yi na tabbatar da tsaro a jihar da bada tabbacin cewa gwamnatin Dikko Raɗɗa za ta cigaba da yin duk abinda ya dace wajen kawo zaman lafiya a jihar.

By ukarofi