Rundunar ‘yan sanda a Jihar Borno ta ɗauki sabbin jami’ai 1,800

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Kimanin sabbin jami’am tsaro (Constables) guda1,800 rundunar ‘yan sanda ta Jihar Borno ta ɗauka aiki domin inganta tsaro a cikin jihar, a cewar kwamishinan ‘yan sanda Abdu Umar.

Da yake bayyana wa manema labarai shirin rundunar, kwamishina Umar ya ce an ɗauki sabbin ma’aikatan ne domin tallafa wa sauran hukumomin tsaro masu tsare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar, haɗi da wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma.

Kwamishina Abdu Umar ya bayyana cewar, a yanzu haka sabbin ɗaukar ‘yan sanda suna samun horaswa dangane da ire-iren rawar da ya kamata su riƙa takawa ta fuskar lamuran tsao a jihar ta Borno.

Umar ya ce bayan horaswar da za su samu, za a rarraba su cikin ƙananan hukumomi ashirin da bakwai na jihar domin lura da lamuran tsaro a sako daga lungu-lungun dake garuruwa, ƙauyuka da unguwannin karkara.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ce ta bijiro sabon tsarin tsaron na al’ummomin karkara da a yanzu haka rundunar tasu ke aiwatarwa, da ya jivanci samar da aiki wa waɗanda suka da ƙoƙari da kuma sha’awar taimakawa wa ayyukan tsaro a karkara.

Kwamishina ya zayyana ayyukan waɗannan sabbin jami’ai da suka haɗa da taimaka wa dakarun ‘yan sanda wajen gano da hana aikata mugayen ayyuka, sasantawa a tsakanin husumai, zaƙulo labarai na sirri kan munanan ayyuka domin gabatar da su wa kwamandojin ‘yan sanda.

Sauran sun haɗa da wanzar da doka da oda, taimakawa jami’an ‘yan sanda kan gudanar da ayyukan su a yankunan karkara, bayar da shawarwarin zaman lafiya wa jama’a, haɗi da gudanar da ayyuka kafaɗa-kafaɗa da masu ruwa da tsaki wajen daƙile aikata laifuka.

“Tuni muka tura jami’an ‘yan sanda guda goma wa kowace ƙaramar hukuma dake cikin jiha domin tallafa wa sauran hukumomin tsaro dake yaƙi da ta’addanci da wasu laifuka.

“Ba da jimawa ba za a ke ganin ‘yan sanda a kowane lungu da saƙo na Jihar Borno. Waɗannan sabbin ɗauke za su riƙa sanya baƙaƙen tufafi, sada da ƙasa, suna da bambancin kayayyaki tsakanin su da ‘yan sanda,” a cewar shi.

Kwamishina ya bayar da tabbacin cewar, ‘yan sanda za su duƙufa farautar maɓuya miyagun mutane domin daƙile aniyyar su ta cutar jama’a.