Shugabancin NDDC: Buhari ya maye gurbin Akwa da Audu-Ohwavborua

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Injiniya Emmanuel Audu-Ohwavborua a matsayin Muƙaddashin Shugaban Hukumar Bunƙasa Neja Delta (NDDC).

Bayanin naɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da Daraktar Yaɗa Labarai ta Ma’aikatar Kula da Harkokin Yankin Neja Delta, Patricia Deworitse ta fitar a ranar Alhamis.

Naɗin Audu-Ohwavborua ya biyo bayan tsige shugaban NDDC mai barin gado, Effiong Akwa da Shugaba Buhari ya yi a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce Audu-Ohwavborua ne zai ci gaba da riƙe hukumar ta NDDC har zuwa lokacin da za a tabbatar da Manajin Darakta da kuma Kwamitin Gudanarwa na hukumar.

Kazalika, sanarwar ta nuna Shugaba Buhari ya amince da a kafa Sabuwar Hukumar Gudanarwar a NDDC.