Putin ya kafa dokar yaƙi a wasu sassan ƙasarsa

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin, ya ce zai kafa dokar yaƙi a yankuna huɗun da Rasha ta mamaye na Ukraine wanda Moscow ta yi iƙirarin cewa yankunanta ne.

Putin ya bayyana haka ne a ranar Laraba a lokacin da yake yi wa Majalisar Tsaron ƙasar jawabi.

Haka nan, Shugaban ya umarci gwamnatin ƙasar ta kafa kwamiti na musmaman ƙarƙashin Firaminista Mikhail Mishustin don yin aiki tare da yankunan Rasha don ƙarfafa wa ƙoƙarin yaƙin Moscow a Ukraine.

Wannan yunƙuri da Putin ya yi na zuwa ne kimanin watanni takwas da ɓarkewar yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine wanda ke nuni da irin kashin da Putin ke shirin sha a hannun sojojin Ukraine.

Putin ya ce matakan da ya ba da umarnin ɗauka za su taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar da masana’antu da sauransu.