Cutar kansa na mayar da yara miliyan guda marayu kowacce shekara – Bincike

Daga AISHA ASAS

Wani binciken masana kimiya ya ce, yara kusan miliyan guda ne a duniya ke rasa iyayensu mata kowacce shekara saboda cutar kansa ko sanqara, abinda ke mayar da su marayu kai tsaye.

Waɗannan alƙaluma an gabatar da su ne a wajen taron cutar sankara ta duniya da ke gudana a Geneva wanda ya nuna alƙaluman yaran da iyayensu mata ke bari a baya sakamakon illar cutar.

Cibiyar Binciken Kansa ta Duniya mallakar Hukumar Lafiya da ke Lyon a Ƙasar Faransa ta gabatar da rahotan binciken da akayi a Afirka, wanda ya shafi mata sama da 2,000 da suka yi fama da sankarar nono a kasashen Namibia da Uganda da Zambia da kuma Najeriya, kuma rabi daga cikin matan sun mutu a cikin shekaru 5.

Jami’in Cibiyar Binciken Valerie McCormak, ya nuna illar cutar a tsakanin mata na dogon lokaci, abinda ya sa suka gabatar da alqaluman da ke nuna cewar tsakanin mata miliyan 4 da suka mutu sakamakon harbuwa da cutar kansa ko sankara a shekarar 2020, yara miliyan guda ne aka bar su ba tare da mahaifiya ba, kuma kashi 45 na adadin sun mutu ne sakamakon cutar sankarar nono ko na mahaifa.

McCormak ya ce, yayin gudanar da binciken a yankin Afirka da ke Kudu da sahara, wasu daga cikin iyalan da matsalar ta shafa sun ce, cutar ta kaiga sayar da filayen da suka mallaka domin neman magani ko kuma samun kulawa a asibiti, abinda ya kai ga mutuwarsu ba tare da barin komai da za a ilmintar da yaransu ba.

Binciken ya kuma bayyana cewar matan da ke tsakanin shekaru 35 zuwa 50 sun fi mutuwa sakamakon cutar saboda ganin cewar suna cikin lokacin haihuwa ne fiye da maza a fadin duniya, yayin da mutanen da ke rayuwa a ƙasashen da aka ci gaba sun fi mutuwa ne lokacin da suka fi yawan shekaru, bayan girman ‘ya’yansu.