Aikin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Sin ya samu Cigaba sosai

Daga CMG HAUSA

Ma Zhaoxu, mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Sin, ya bayyana a yau Alhamis, a wajen wani taron manema labaru da ya gudana cikin cibiyar kafofin watsa labarai ta taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin karo na 20 cewa, aikin hulɗa da ƙasashen ƙetare na ƙasar Sin ya samu ci gaba matuƙa, cikin shekaru 10 da suka wuce, inda yawan ƙasashen da ta ƙulla hulɗar diflomasiyya da su ya karu daga 172 zuwa 181.

Jami’in ya nanata babban maƙasudin aikin hulɗa da ƙasashen waje na ƙasar Sin, wato ƙoƙarin kare zaman lafiya a duniya, da neman samun ci gaba tare da sauran ƙasashe, don kafa wata al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai ɗaya.

Ban da wannan kuma jami’in Sin ya ce, ƙasarsa na adawa da matakan saka wa wasu ƙasashe takunkumi bisa ra’ayi na ƙashin kai, da matsawa sauran ƙasashe lamba don tilasta musu bin umarni, kana sam ba za ta yarda ba, da yadda wasu ɓangarorin ke neman tsoma baki cikin harkokin gidan Sin, ta hanyar fakewa da batun kare haƙƙin ɗan Adam.

Mai fassara: Bello Wang