Manhaja
Blueprint
Hukumar Daraktoci, Hukumar Gudanarwa da Ma’aikatan kamfanin Blueprint Newspapers Limited, Mawallafan jaridun Blueprint, Blueprint Weekend, Manhaja (wacce ake wallafawa da harshen Hausa) da jaƙaƙurin sashen yanar gizo (na Blueprint da Manhaja) muna masu yi dukkan abokan huldarmu gaisuwar Sabuwar Shekara.
Muna masu yin amfani da wannan dama wajen. Bayyana matuƙar godiya da jin daɗinmu ga makarantanmu da kuma kwastomominmu, waɗanda suka ba mu goyon baya da taimako ta hanyar ba mu talla a cikin shekara ta 2025.
Kasancewar ku tare da mu ya fi duniya da abin da ke cikinta a gare mu kuma girmamawa ce gare mu da ku ka kasance cikin wannan tafiya da ,mu. Muna ƙara miƙa godiyarmu bisa zaɓen Blueprint Newspapers a matsayin tushe samun labarai, rubutu, bincike da talla da ku ke ɗaukar nauyi.
A yayin da muke shiga cikin sabuwar shekara ta 2026, muna yi muku fatan farin ciki, wadata da cimma nasara. Allah Ya sa burinku ya cika a yayin da ku ke fafutukar ganin kun cimma muradanku. Za mu ci gaba da kawo muku rahotonni masu inganci da saƙonni masu ilimintarwa, nishaɗantarwa da ƙarfafa gwiwar makarantanmu.
Muna masu ƙara gode muku bisa amincin da ku ka bai wa jaridun Blueprint da Manhaja.
Muna masu fatan ci gaba da ƙara himmatuwa wajen yi muku hidima a 2026 da bayan hakan.
Sa hannu:
Hukumar Gudanarwa
Barka da
Sabuwar Shekara
