*Wadata za ta farfaɗo bayan fara aiwatar da sabbin dokokin haraji – Tinubu
*Bankuna za su fara cire N50 duk N10,000
*Sauya dokokin haraji bayan amincewar majalisa tamkar yin takardun bogi ne – Atiku
*Za a samu raguwar hauhawar farashi zuwa kashi 12.94, inji Bankin CBN
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, shekarar 2026 za ta zama farkon wani sabon mataki na ƙarfin bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya, yana mai jaddada cewa, sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar sun fara haifar da sakamako mai amfani ga talakawan ƙasa.
A cikin saƙon sabuwar shekara da ya aikawa ’yan Nijeriya a ranar 1 ga Janairu, 2026, Shugaban ƙasar ya ce Nijeriya ta rufe shekarar 2025 cikin kwarin gwiwa ta fuskar tattalin arziki duk da matsin lambar tattalin arzikin duniya.
Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta ƙara gina kan nasarorin da aka riga aka samu tare da mayar da hankali kan bunƙasuwar da ta shafi kowa, ingantaccen tsaro da kuma tsauraran matakan kuɗi.
Yayin da yake taya ’yan Nijeriya murnar shiga sabuwar shekara, Tinubu ya nuna godiya ga Allah tare da sake jaddada imaninsa ga ƙarfin haɗin kan al’umma wajen gina ƙasa mai wadata, juriya da kwanciyar hankali.
A cewarsa, Nijeriya ta samu ci gaba mai yawa a shekarar 2025 biyo bayan sabunta tsarin kuɗi da ci gaba da manyan sauye-sauyen tsari a tattalin arziki. Ya bayyana cewa ƙasar ta samu bunƙasar tattalin arzikin cikin gida a shekarar, inda ake sa ran ci gaba da bunƙasar sa a shekara na gaba.
“Ina mai tabbatar muku cewa a shekarar 2026, za mu ƙara rage hauhawar farashi tare da tabbatar da cewa ribobin sauye-sauyen nan sun kai ga kowane gidan ’yan Nijeriya,” inji Tinubu.
Shugaban ƙasar ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tsauraran matakan kuɗi domin ɗorewar tattalin arziji na dogon lokaci. Ya tunatar da cewa kwanan nan ya gabatar da ƙudirin Kasafin Kuɗin 2026 ga Majalisar ƙasa, yana mai cewa muhimman sauye-sauyen nan na shimfiɗa tubalin wadata mai ɗorewa.
Dangane da haraji, Tinubu ya yi tir da yawaitar haraji a sassa daban-daban na ƙasa tare da yaba wa jihohin da suka rungumi tsarin daidaita haraji ta ƙasa domin rage wa ’yan ƙasa da ’yan kasuwa nauyin haraji da kuɗaɗe. Ya ce shekarar 2026 za ta zama muhimmiyar shekara wajen aiwatar da sauye-sauyen haraji da za su samar da adalci, gasa mai kyau da tsarin kuɗi mai ƙarfi.
A ɓangaren tsaro, Shugaban ƙasar ya amince cewa ci gaban tattalin arziki ba zai yiwu ba tare da zaman lafiya da tsaro ba. Ya bayyana cewa, tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa ciki har da Amurka, an kai manyan hare-hare kan wuraren ’yan ta’adda a wasu sassan Arewa maso Yamma a ranar 24 ga Disamba, tare da ci gaba da ayyukan soji a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Ya ce, a shekarar 2026 hukumomin tsaro da leƙen asiri za su ƙara zurfafa haɗin gwiwa da na yankin da na duniya domin kawar da barazanar tsaro. Haka kuma, ya sake jaddada goyon bayansa ga tsarin ’yan sanda na rarraba iko, tare da tsauraran ƙa’idoji, da kuma kafa jami’an tsaron gandun daji yadda ya dace domin tinkarar ta’addanci, fashi da makami da sauran laifuka.
A ƙarshe, Shugaban ƙasar ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su mara wa gwamnatinsa baya, yana mai cewa gina ƙasa nauyi ne na kowa. Ya bukaci haɗin kai, kishin ƙasa da rikon amana, tare da yi wa ’yan ƙasa fatan samun sabuwar shekara mai cike da zaman lafiya, aiki tuƙuru da wadata, yana kuma roƙon Allah ya kare Nijeriya da jami’an tsaronta.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta janye ko dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji ba, yana mai jaddada cewa za a fara cikakken aiki da su daga ranar 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara tun farko.
Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, inda ya ce duk da ce-ce-ku-ce da muhawara da suka biyo bayan dokokin, gwamnati ta yanke shawarar ci gaba da aiwatar da su, domin a cewarsa lokaci ya wuce na tattaunawa, yanzu kuma lokaci ne na aiwatarwa.
Sabbin dokokin harajin sun fuskanci suka daga wasu ɓangarori na jama’a, musamman kan zargin cewa za su ƙara wa talakawa nauyin biyan haraji.
Sai dai Shugaba Tinubu ya musanta hakan, yana mai cewa manufar dokokin ba wai ƙara haraji ba ce, illa sake gina tsarin haraji na ƙasa ta yadda zai zama adali, mai sauƙi da kuma amintacce.
Shugaban ƙasar ya bayyana gyaran harajin a matsayin wata dama ta musamman wadda ba kasafai ake samu ba, domin gina tubalin tattalin arziki mai ƙarfi da adalci.
Ya ce dokokin za su taimaka wajen daidaita dokoki daban-daban da ke aiki a baya, rage rikice-rikice, da kuma inganta alaƙa da amincewa tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa.
A cewarsa, duk da hayaniyar da ake yi kan yiwuwar sauya wasu sashe na dokokin, babu wata matsala mai nauyi da aka gano da za ta sa a dakatar da tsarin ko a rushe shi. Shugaban ƙasar ya gargadi jama’a kan ɗaukar matakai cikin gaggawa, yana mai cewa amincewa da gwamnati na ginuwa ne a hankali, ta hanyar tsayayyen matsaya da bin ƙa’ida.
Tinubu ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa na mutunta doka da oda, tare da kiyaye mutuncin dokokin da aka riga aka amince da su. Ya ce zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Majalisar Dokoki ta ƙasa domin magance duk wata matsala ta gaske da ka iya tasowa yayin aiwatar da dokokin.
Shi kuwa Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya gargaɗi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yiwuwar ɓarkewar rikicin tsarin mulki, bayan bayyanar cewa sigar dokokin haraji da aka wallafa a kundin gwamnati ba ta yi daidai da abin da Majalisar Dokoki ta amince da shi ba.
Atiku ya bayyana lamarin a matsayin haramtacce kuma wanda ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, yana mai jaddada cewa duk wata doka da aka wallafa ba tare da bin abin da majalisa ta zartas ba, babu inganci a kanta, kuma ba ta da ƙarfin doka.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a daren Lahadi, Atiku ya ce tabbatarwar da Majalisar Dattawa ta yi cewa akwai saɓani tsakanin dokokin harajin da aka zartar da kuma sigar da aka wallafa, abin damuwa ne mai girma da ke tabo mutuncin tsarin dokoki na ƙasa.
A cewarsa, “Tabbatarwar Majalisar Dattawa cewa dokar harajin Tinubu da aka wallafa ba ta dace da wadda Majalisar ƙasa ta amince da ita ba, babbar matsala ce ta tsarin mulki. Dokar da ba a zartas da ita a irin wannan tsari ba, ba doka ba ce kwata-kwata.”
Shi kuwa, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin ƙasar zai samu bunƙasa mafi kyau a shekarar 2026, tare da sauƙaƙewar hauhawar farashi, sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki, ƙaruwar amincewar masu zuba jari da kuma sauƙaƙa manufofin kuɗi.
CBN ya bayyana hakan ne a cikin rahoton ‘Macroeconomic Outlook for Nigeria’, 2026 da bankin ya fitar ranar Talata.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ya nuna alamun ja baya a shekarar 2025, inda bunƙasarsa ta ragu zuwa kashi 3.20 daga 3.30 a 2024, sakamakon taaaddamar kasuwanci da raunin buƙatar kaya da ayyuka.
Sai dai rahoton ya nuna cewa, hauhawar farashin duniya ta lafa zuwa kashi 4.20% abin da aka danganta da raguwar farashin makamashi da inganta hanyoyin samar da kayayyaki.
A cewar CBN, ana sa ran tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da faɗaɗa, inda ake hasashen bunƙasa da kashi 4.49 a shekarar 2026. Bankin ya ce wannan hasashe ya ta’allaƙa ne kan ribar sauye-sauyen tsarin tattalin arziki da aka aiwatar a fannoni da dama, tare da sassauta manufofin kuɗi a hankali.
CBN ya ce waɗannan matakai za su inganta yanayin kasuwanci, su ƙara jawo masu zuba jari, tare da bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar ja ragamar bunƙasar tattalin arziki.
A wani batun tattalin arzikin kuwa, Bankuna a Nijeriya za su fara cire naira 50 a matsayin harajin da banki ke cirewa kan kuɗin da aka tura ko aka cire da ya wuce naira 10, 000 daga ranar 1 ga Janairun 2026 bisa sabuwa dokar haraji da aka kafa.
An sanar da hakan ne a cikin wasiƙu da bankuna suka aika wa kwastomominsu kafin fara aiwatar da wannan sabon tsarin.
Harajin yana nufin cire naira 50 kai tsaye a kan kowanne kuɗi da ya shiga ko ya fita daga cikin asusun banki da ya wuce naira 10,000.
Wannan tsarin ba zai shafin kuɗin albashin mutum da ke shiga asusun bankinsa ba da kuma kuɗin da aka tura daga banki iri ɗaya.
A da, wanda aka tura wa kuɗi kaɗai ake cirewa wannan harajin, amma yanzu tsarin zai shafi wanda ya tura kuɗin ma.
Bankunan sun fayyace cewa wannan harajin ya bambanta da harajin da bankuna ke yi da aka saba gani kuma za a nuna wa mutum a lokacin da yake tura kuɗi.
